Hedikwatar tsaro ta Nijeriya ta tabbatar da bayyanar wata sabuwar ƙungiyar ‘yan ta’adda da ake kira ‘Lukarawas’ wadda ke ƙara haifar da matsalar rashin tsaro a yankin Arewa maso Yamma na Nijeriya.
Daraktan harkokin watsa labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a kan ayyukan sojoji a ranar Alhamis a birnin Abuja.
Janar Buba ya bayyana cewa wannan sabuwar ƙungiya ta ‘yan ta’adda ta fito ne daga Jamhuriyar Nijar bayan juyin mulki wanda ya kawo cikas ga haɗin gwiwar tsaro tsakanin Nijeriya da Nijar.
Ya ce ‘yan ta’addan sun fara kutsawa cikin yankin Arewacin jihohin Sokoto da Kebbi daga ɓangaren Nijar da Mali, musamman bayan juyin mulki a Jamhuriyar Nijar.
A cewarsa, kafin juyin mulkin, ana gudanar da aikin haɗin gwiwa a iyakar ƙasashen tare da jami’an tsaron.
Janar Buba ya ce mutanen yankin sun ba da mafaka ga ƙungiyar suna tsammanin sun zo musu da alheri, lamarin da ya sa suka kasa kai rahoto ga sojoji da hukumomin tsaro.
Ya tabbatar da cewa sojojin sun ci gaba da gudanar da leken asiri, sa ido, da kuma tattara bayanai don kawar da ‘yan ta’addan.