Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, har yanzu shi mamba ne a Jam’iyyar All Progressiɓe Congress (APC), kuma zai yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta samu babban tagomashi.
Buhari ya bayyana haka ne a cikin wata takardar sanarwa da mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya sanya wa hannu, kuma aka raba wa manema labarai jiya Alhamis.
Wannan ya biyo bayan hirar da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna kuma na hannun damansa, Malam Nasir El-Rufai ya yi ne, inda ya ke cewa, bai bar APC ba sai da Buhari ya sanya masa albarka.
Garba Shehu ya ce, “Ba tare da yin la’akari da wani ba, ko wani fitaccen mutum, ko al’amura, ƙa’idoji da aƙidu da shugabannin jam’iyyar a matakai daban-daban ke tattaunawa a halin yanzu ba, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya nanata abin da ya sha faɗa ba adadi, cewa shi ɗan Jam’iyyar APC ne. Kuma yana son a kira shi da ɗan jam’iyya mai aminci.”
Ya ce, yana son ya fitar da kowa a cikin shakkun cewa, ba zai taɓa juya wa jam’iyyar da ta ba shi wa’adi biyu baya ba, kuma zai yi duk abin da zai iya domin ganin ta samu babban tagomashi.
“Ni ɗan Jam’iyyar APC ne kuma ina son a yi min magana kamar haka. Zan yi ƙoƙarin ganin jam’iyyar ta shahara ta kowace hanya.”
Ya ci gaba da cewa, a halin yanzu babu abin da ya ke da shi illa godiya ga irin goyon bayan da Jam’iyyar ta ba shi a baya da kuma lokacin da yake Shugaban ƙasa, wanda a ganinsa a matsayin mafi girman daraja, kuma ba zai taɓa neman wani abu ba.
Ya ci gaba da cewa, irin gwagwarmayar da waɗanda suka kafa jam’iyyar suka sha don kare tsarin mulkinmu, da dimokuraɗiyya a matsayin tsarin gwamnati, sadaukarwa ce da ta dace da ya kamata a kiyaye da kuma raya ta.