Hirar Ladin Cima: MOPPAN da AFMAN sun jagoranci sulhu tsakanin Naziru Sarkin Waƙa da sauran ‘yan fim

Daga WAKILINMU

A jiya Litinin 14 ga Fabrairun 2022 ne, ƙungiyar MOPPAN tare da haɗin gwiwar ƙungiyar AFMAN da kuma Kwamitin Dattawan Kannywood suka yi zaman sulhu tsakanin ‘ya’yan masana’antar da suka sami rashin fahimta sakamakon hirar Hajiya Ladin Cima da BBC Hausa ta watsa kwanan nan.

Zaman da aka yi a zauren taron Kannywood TV da ke Kano, ya samu halartar shugabannin ƙungiyoyin MOPPAN da na AFMAN da shugabannin ƙungiyar mata na ‘K-WAN’ da kuma dattawan Kannywood.

Daga cikin Dattawan da suka halarci taron, akwai akwai, Malam Auwalu Masha, Mai’unguwa Ibrahim Mandawari, Ibrahim Gumel, da Kabiru Maikaba.

Sanarwar da Kakakin MOPPAN na Ƙasa, Al-Amin Ciroma ya fitar ta nuna taron ya tattauna abubuwa da dama, wanda daga baya aka yi nasiha da jankunne gami da faɗakarwa daga malamai.

Haka kuma, taron ya yi bayanai na girmamawa ga Hajiya Ladin Cima da irin gudunmawar da ta bayar ga masana’antar fim, da kuma ci gaba da lallashinta da girmama dukannin dattijan masana’antar da guje wa yin lafazi maras kyau a kansu.

Shi ma Shugaban AFMAN, Alhaji Sani Sule Katsina, ya jaddada kira wajen kauce wa maganganu barkatai a kafafen sadarwar zamani na soshiyal midiya. Ya ƙara da cewa, “Sai bango ya tsage ƙadangare ke samun wajen shiga.”

A ganinsa, ‘yan fim ɗin ne ke bai wa ‘yan jarida da mutanen gari damar maganganun da ba su dace ba a kansu.

An dai yi kira da a samar da bita ta wayarwa da ilimantarwa a kan amfani da Soshiyal midiya, domin guje wa irin haɗarin da za ta iya samarwa.

An buƙaci a riƙa yi wa juna uzuri kuma a daina yin magana ko aika saƙonni cikin fushi.

Bayan bayanai masu ratsa jiki da nasihohi da taron ya samar ne, ƙungiyar matan Kannywood, Mai suna ‘K-WAN’, ta janye iƙirarin maka Naziru M. Ahmad (Sarkin Waƙar Sarkin Kano) a kotu, ta kuma nemi a guji yin lafuzzan da suke taɓa darajar mata a Kannywood.

Bayan wannan bayanan na kungiyar ‘K-WAN’ ɗin ne shi ma Nazir Ahmad, ya yi tsokaci bisa rashin fahimtar bayanansa da ba a yi ba, inda ya bada haƙuri kuma ya nemi a haɗa kai a samar da ƙa’idojin yin magana a kafafen sadarwar zamani.

Hakan ta sa aka sake yin kira ga duk ‘ya’yan wannan masana’anta da su dakatar yin duk “posting” mai alaƙa d
da wannan saɓanin face bayanin sulhu.

Shugaban Ƙungiyar MOPPAN na Ƙasa, Dr. Sarari ya sanar da mahalarta taron cewa MOPPAN na daf da shirya taron bita, domin wayarwa da ‘yan masana’antar da ilimantar da su yadda ake amfani da soshiyal midiya da kuma irin haɗurran da suke tattare da ita.

Mahalarta taron su ne: Auwalu Ismail Mashal; Hon. Mustpha Naburaska (S.A ga Gwamnan Kano kan sha’anin Kannywood); Mohammad Ibrahim Gumel; Salisu Muhammad Officer; Hadiza Muhammad; Abubakar Bashir Maishadda; Hannatu Bashir; Hauwa A. Bello.

Sauran sun haɗa da Kamal S. Alkali; Mubarak Abba; Misbahu M. Ahmad; Naziru M. Ahmad; Muhammad Kabiru Maikaba; Alhaji Ibrahim Mandawari; Alhaji Sani Sule Katsina (Shugaban AFMAN na ƙasa) da kuma Dr. Ahmad Mohammed Sarari (Shugaban MOPPAN na ƙasa).