Hisbah ta ƙwace kwalaben giya 1,906 da kama mutum 92 a Jigawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Hisbah ta jihar Jigawa ta ce ta ƙwace kwalaben giya 1,906 a sumamen da ta kai a lokuta daban-daban a faɗin jihar a shekarar da ta gabata, 2021.

Kwamandan rundunar, Mallam Ibrahim Dahiru, shi ne ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya, NAN, a Dutse, babban birnin jihar, a ranar Talatar makon jiya.

Mallam Ibrahim ya ce sun yi nasarar ƙwace giyar ne a otal-otal da wuraren shan barasa daban-daban a faɗin jihar.

Shugaban Hisbar ya kuma ce sun kama mutum 92 da suke zargi da aikata laifuka na baɗala daban-daban, waɗanda suka haɗa da karuwai a lokacin sumamen nasu.

Laifukan da ake zargin mutanen sun aikata sun haɗa da caca da yawon-ta-zubar da shirya liyafar casu a lokacin biki da sauransu, in ji kwamandan. Haka kuma ya ce a tsawon lokacin hukumar ta Hisbah ta rufe gidajen karuwai.

Malam Ibrahim ya qara da cewa an miqa kwalaben giyar da aka ƙwace da mutanen da aka kama ga ‘yan sanda domin ƙara bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *