Hisbah ta cafke waɗanda ake zargi da yunƙurin auren jinsi a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Hukumar Hisba ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Sheikh Aminu Daurawa, ta ce ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da yunƙurin shirya auren jinsi a jihar.

Rahotanni sun nuna cewa Kwamandan Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a ranar Asabar.

Ya bayyana a wani faifan bidiyo cewa an ga wasu samari biyu masu suna Khalifa da Abubakar suna ƙoƙarin sumbatar juna a yayin wani biki, wanda ake zargin bikin aurensu ne.

Sai dai waɗanda ake zargin sun musanta zargin, inda suka ce taron bikin ranar haihuwa ne da bikin aure ba kamar yadda ake zargi ba.

A cewar d’ɗaya daga cikin waɗanda ake zargin, khalifa, shi ne ya shirya bikin zagayowar ranar haihuwarsa, sai abokinsa Abubakar ya ba shi kek a baki ta hanyar amfani da bakinsa.

Kazalika, Daurawa ya ce mutane biyun suna hannunsu, kuma ana ci gaba da gudanar da bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *