Hisbah ta tallafa wa matan da suka tuba daga harkar baɗala a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Mu’assasatul Khairiyya tare da haɗin-gwiwar Hukumar Hisbah a Jihar Katsina, sun gudanar da taron yaye mata goma da suka shiriya daga harkokin baɗala tare tallafa musu don samun kafar rayuwa mai tsafta.

Da yacke gabatar da jawabi a taron, Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, Dakta Aminu Usman Abu Ammar, ya ce matan da aka tallafa wa sun kasance daga cikin waɗanda hukumar ke kira da yi masu nasiha kan ɗabi’un rayuwa mai kyau. Ya ce, “A tsawon lokaci, hukumar Hisbah ta cigaba da yi musu wa’azi da shawara, amma sai aka ga dacewar tallafa masu.”

Ya kuma ce, Hajiya Hauwa Umar Raɗɗa ta ɗauki nauyin ɗawainiyarsu, don ganin sun samu dama ta cikakkiyar natsuwa da koyarwa.

A nasa jawabin, Mataimakin Gwamnan jihar, Alhaji Farouk Lawal Joɓe, ya yaba da aikin na taimako da ƙungiyoyin suka yi, tare da nuna goyon bayansa ga ƙoƙarin da hukumar ke yi wajen hana aikata munanan ɗabi’u a cikin al’umma.

Ya kuma yi kira ga iyaye su mayar da hankali wajen tarbiyyar ƴaƴansu don rage yawaitar abubuwan da ke kawo lalacewar al’umma.

Bayan ga haka, an bada tallafi na musamman ga matan, ciki har da kekunan ɗinki ga mata guda uku da injinan markaɗe ga mata guda bakwai, tare da kayan karatu kamar Ƙur’ani da wasu abubuwan ibada.

Haka nan, an kuma raba masu abayu, turamen atamfa, da buhunan fulawa domin taimakawa wajen farfaɗo da rayuwarsu.

Har’ilayau, Mu’assasatul Khairiyya ta ba kowacce tallafin Naira 100,000.
Mataimakin Gwamnan ya ba su kyautar Naira dubu ɗari-ɗari a matsayin ƙari.

Malamai da shugabannin addini sun yi wa matan nasiha, inda suka bukaice su da su kiyaye mutuncinsu da na addininsu tare da tabbatar da tabbatacciyar tuba da bin sahihin hanya.

An yi addu’ar cewa su zama masu tsayin daka wajen gudanar da lamuransu cikin tsafta da ƙaunar zaman lafiya a cikin al’umma.