Honda da Nissan sun sanar da yin haɗaka a Fabrairu 

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kamfanonin ƙera motoci na Honda da Nissan na shirin bayyana haɗaka da za su yi a tsakiyar watan Fabrairu, kamar yadda jami’an kamfanin suka bayyana a ranar Juma’a.

Kamfanonin ƙera motoci biyu, na biyu mafi girma na Japan da na uku a duniya, a baya sun sanar da shirye-shiryen haɗewa a ƙarƙashin wani kamfani a cikin 2026 kuma da farko sun yi niyyar bayyana hakan ne a ƙarshen Janairu amma daga baya hakan ya ci tura.

A cewar majiyoyin da ke da masaniya kan lamarin, kamfanin na Honda na ci gaba da matsa wa kamfanin Nissan don ƙara ƙaimi wajen sake fasalin tsarin.

A watan Nuwamba, Nissan ya sanar da shirin rage guraben ayyukan yi 9,000 a duk duniya tare da rage ƙarfin samar da kayayyaki a duniya da kashi 20 cikin 100 bayan da ya ba da rahoton faɗuwar sama da kashi 90 cikin 100 na ribar da aka samu a tsakanin watan Afrilu zuwa Satumba.

A halin yanzu, kamfanin Mitsubishi, abokin tarayya na Nissan, ya daɗe yana tunanin shiga cikin haɗakar amma yanzu ya karkata ga ci gaba da zaman kansa, inji majiyoyin.