HOTUNA: Adamu ya ƙaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen Jihar Osun

Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC don zaɓen gwamna da zai gudana a Jihar Osun.

An kafa kwamitin ne ƙarkashin jagorancin Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas da takwaransa na Jihar Kano, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

Sai dai, Gwamna Sanwo-Olu bai samu halartar bikin ƙaddamarwar ba sakamakon wani aikin ƙasa da ya ɗauke shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *