A yau Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya maƙala wa dogarinsa (ADC), Lt. YM Dodo sabon matsayinsa na ‘Colonel’. Buhari ya yi hakan ne tare da taimakon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo da maiɗakin Dodo.
Wannan taƙaitaccen biki ya gudana ne gabanin soma Taron Majalisar Tasaro ta Ƙasa a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.