Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa wa jarumi a masana’antar Kannywood, Abba El-Mustapha, takardar naɗin da ya yi masa kwanan nan.
Gwamna Abba ya naɗa El-Mustapha ne a matsayin Babban Sakataren Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar.
Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Dr Abdullahi Baffa Bichi shi ne ya miƙa wa El-Mustapha takardar a madadin Gwamna Abba.
Ga ƙarin hotunan yadda taron miƙa takardar ya kasance:



