HOTUNA: Yadda masoya suka yi dandazo wurin karɓar shaidar lashe zaɓen Abba Kabir

A ranar Laraba Hukumar INEC ta miƙa wa ‘yan takarar da suka lashe zaɓen gwamna a jihohinsu shaidar lashe zaɓen gwamnan da ya gudanar ranar 18 ga Maris, 2023.

Haka ma lamarin ya kasance a Jihar Kano, inda ɗan takarar Jam’iyyar NNPP, Abba Kabir da Mataimakinsa, Aminu Abdussalam, suka karɓi shaidar lashe zaɓe a matsayin gwamna da mataimakinsa daga hannun INEC.

Masoya daga sassan jihar suka fito don nuna goyon baya da murnar ga Gwamnan Kano mai jiran gado da mataimakinsa yayin da suka karɓi shaidar lashen zaɓen.

Ga ƙarin hotunan irin wainar da aka toya daga Sani Maikatanga: