HOTUNA: Yadda taron maulidin Sheikh Ahmad Tijjani karo na 6 ya gudana a Lafiya

Daga ISAH BASHIR

A ranar Lahadin da ta gabata dubban mabiya Ɗariƙar Tijjaniya ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi, suka gudanar da babban taron maulidi da suka saba shiryawa duk shekara karo na shida a garin Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa.

Taron wanda aka gudanar a dandalin Lafia Squre, ya samu mahalarta daga ciki da wajen Nijeriya.

Gwamnan jihar Nasarawa, Injiniya Abdullahi A. Sule, da Sarkin Lafiya, Mai Martaba Jastis Sidi Bage, da Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi da sauransu, na daga cikin waɗanda suka halarci taron.

Yayin da Gwamna Sule ke gaisawa da Sheikh Ɗahiru Bauchi a wajen taron
Yayin da Sarkin Lafiya, Sidi Bage ke gaisawa da Sheikh Ɗahiru Bauchi a wajen taron
Yayin da Gwamna Sule ke jawabi a wajen taron

Sa’ilin da Sheikh Ɗahiru Bauchi ke jawabi