Huawei zai taimaka wa ƙoƙarin Kenya na faɗaɗa kayayyakin sadarwar intanet

Daga CMG HAUSA

Katafaren kamfanin sadarwa na ƙasar Sin Huawei, zai haɗa hannu da gwamnatin ƙasar Kenya wajen bunƙasa tsarin sadarwar ta hanyar faɗaɗa kayayyakin samar da su.

Kamfanin ya ce zai shimfida manyan wayoyin sadarwa na fiber cables masu tsawon kilomita 43,000 a fadin ƙasar domin bunƙasa sadarwar intanet.

Daraktan sashen harkokin kasuwanci na kamfanin Huawei a Kenya, Steve Kamuya, ya ce samar da hanyoyin sadarwar, zai fara ne da shimfiɗa kilomita 25,000 na wayar fiber mai haɗe manyan yankunan da ƙananan yankunan ƙasar ta hanyar haɗin gwiwa da hukumar kula da fasahar sadarwa ta ƙasar.

Ya ƙara da cewa, daga baya kuma, za a shimfiɗa ƙarin wayar fiber mai tsayin kilomita 18,000 na ƙarin ingancin sadarwar intanet, a wani ƙoƙari na cike giɓin dake akwai a ƙasar.

Ita kuwa mataimakiyar daraktan sashen shirye-shirye na kamfanin Huawei a Kenya, Maureen Mwaniki cewa ta yi, zuba jari a kayayyaki masu amfani da inganta basira, shi ne jigon cike gibin dake akwai a ƙasar.

Ta ce kamfanin Huawei ya gabatar da shirye-shirye a Kenya da nufin bunƙasa ilimin fasahar zamani a tsakanin matasan ƙasar domin tabbatar da ana damawa da su wajen raya tattalin arziki dake mai da hankali kan ilimi.

Fassarawa: Fa’iza Mustapha