Hubbaren Shehu Ɗanfodiyo: Wurin da ba ya rasa masu ziyara

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato

Hubbaren Shehu Usmanu na ɗaya daga cikin wuraren tarihi na Daular Usmaniyya da aka kafa fiye da shekaru 200, da jihar Sakkwato da Sakkwatawa ke alfahari da wurin mai daɗaɗɗen tarihi.

Ɗaruruwan al’umma daga sassa daban-daban na duniya ne dai ke kai ziyara a kusan ko wace sa’a, kuma kowace rana da dama na neman tubarakki.

Shehu Usmanu Ɗanfodiyo dai ne ya kafa daular da ta yi fice a nahiyar Afirika musamman a jihohin Najeriya wajen jaddada addininin Musulunci.

Ƙofar shiga Hubbare

Wakilin Manhaja a Sokoto, Aminu Amanawa ya ziyarci hubbaren inda ya zanta da mai buxe hubbaren, daman za a ga wasu daga cikin wuraren tarihin da ke a hubbaren.

Wurin na cikin ƙwaryar birnin Sakkwato ne, kuma a cewar mai buɗe Hubbaren Shehu Usmanu, Alhaji Bala Ibrahim, Hubbaren Shehu Usmanu maƙabarta ce da aka bizne salihan bayin Allah da suka yi hidima wajen kafa Daula mafi qarfi a nahiyar Afirika, watau Daular Usmaniya.

“Ainihi dai Hubbare gida ne na Sheikh Usmanu Ɗanfodiyo, bayan an ƙare jihadi yana sifawa ya umarci ɗansa Muhammadu Bello da ya gina masa gida da masallaci, shine ɗan nasa ya gina masa gidan, sannan daga yamma da wannan Hubbare, ya gina masa masallaci wanda yanzu ake kira da Masallacin Shehu, kuma bayan ya taso ya zauna shekara biyu a gidan, sai ya koma ga mahaliccinsa, to nan ne Hubbare,” inji mai buɗe Hubbaren.

Bayan rasuwar jagoran jihadin Daular Usmaniyya anan aka bizne shi a ɗakin matarsa Hauwa’u, mahafiya ga sarkin musulmi Muhammadu Bello da Atiku, kuma yana tare da ‘ya’yansa biyu, Muhammadu Sambo da Hassan.

A cewar mai buɗe Hubbare, Hubbaren wuri ne da ake bizne muhimman mutanen da suka riga mu gidan gaskiya, kuma wuri ne na Torankawa zuri’ar Shehu Usmanu Ɗanfodiyo, amma ana bizne mutanen da suka nemi alfarma ga sarkin musulmin Daular Usmaniyya.

“Mafi yawan waɗanda aka bizne sarakunan Musulunci ne, bayan Shehu Usmanu, akwai na Sarkin Musulmi Amadun Rufa’i, Sarkin Mu’azu Ɗan Bello, Sarkin Musulmi Hassan Ɗan Mu’azu, Sarkin Musulmi Abubakar na III, Sarkin Musulmi Attahiru II, Sarkin Musulmi Muhammadu Amadu Mai Turare, Sarkin Musulmi Muhammadu Macciɗo, da kuma Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuƙi, duka waɗannan anan Hubbare aka bizne su, kuma kaburburansu na nan ciki.”

Maƙabartar Hubbare dai an samar da ita ne tun lokacin ƙaurar Shehun Usmanu sama da shekaru 200 kenan, amma baya ga sarakuna da akwai wasu muhimman mutanen da suka rasu aka bizne su a Hubbaren Shehu?
Eh akwai irin su Ummaru Ali Shinkafi, tsohon gwamnan Sakkwato Garba Na Dama, Tafidan Sokoto, da sauransu da damar gaske duk anan aka bizne su.

Tarin jama’a daga ƙasashen duniya da dama ne dai ke kai ziyara a wannan Hubbare, kama daga Turawa, Larabawa, amma a cewar Alhaji Bala Ibrahim Jamhoriyyar Nijar da wasu jihohin arewa maso gabas ne suka fi kai ziyara a wajen.

“Jihohi irinsu Adamawa, Bauchi, Gombe, Kano, sun fi kai ziyara a wannan Hubbaren, baya ga irin amare da ake kai idan za a aurar da su, domin ziyara, wannan na daga cikin karamar da Shehu Ɗanfodiyo ya samu.”

Da shigarka Hubbaren dai za ka ci karo da ginin makarantar da Shehu Usmanu ke karantar da ɗalibansa da ake kira ‘Jangirde’, wucewarka wajen ke da wuya za ka soma cin karo da dattawa a zaune suna jiran sadaka daga masu kai ziyara a Hubbaren.

Koda yake galibin masu ziyarar kan fito daga jihohi da dama musamman na Arewa maso gabas, amma kuma akwai amaren da ke zuwa Hubbaren da dattawa domin neman tubarraki da samun zaman lafiya a gidajen aure, da dama kuma na zuwa don neman ‘ya’ya na gari, ɗaya daga cikin jagoran da ke kai amare wajen ta bayyana sunanta da, Uwar Suwaiba daga Ruggar Dubu ta ƙaramar hukumar mulkin Dange-shuni, ta ce, suna ganin haske ga duk amaren da ake aurarwa da suka ziyarci Hubbaren.

Ta ƙara da cewa, “muna kawo amarya ne domin neman tubarraki, mun sha kawo amare kuma da akwai haske sosai, za ka ga amaren da muka kawo nan suna cikin kwanciyar hankali da mazajen su, sun kuma samu yara masu albarka, kuma tun tashi na ni dai ba wata amarya ta ƙauyen Ruggar Dubu da ba a kawo ta nan ba kafin aurar da ita.”

Hubbaren dai na da ɓangarori da dama inda Kubba, wajen da kabarin Shehu Usmanu yake da ‘ya’yansa biyu, Muhammadu Sambo da Hassan, inda baya ga ɗakin da kaburbura nasu suke, arewa ga wajen kuma akwai wata runfa da ke ɗauke da jerin kaburbura goma.

Rukunin wasu masu ziyara

Na farko daga yamma kabarin Abdurahman ne daga Hadiza ‘yan shehu Usmanu, sai sahibin Shehu Usman Liman Abubakar, yayin da kabari na 3 daga yamma na kwamandan sane, watau sarkin yaƙi Aliyu Jodi, sai Kabarin Muhammadu Mai Fulani dan sarkin musulmi Amadun Rufai jika ga Shehu Usmanu, sai Amadun Ɗan Atiku, Hodiyo, Muhammadu Mudagel tare da Aishatu ‘ya’yan Muhammadu Mu Alkammu, sai Sarkin Musulmi Amadun Rufai tare da Nana Asma’u ‘ya’ya ga Shehu Usmanu, sai ƙarshe kabarin Sarkin Musulmi Hassan Ɗan Mu’azu da Sarkin Musulmi Abubakar na III.

Hakama daga cikin abubuwan tarihin da ke Hubbaren har da shantalin Shehu, da yake amfani da shi wajen sanya rowan sha, kuma shantalin a cewar ɗaya daga cikin masu jagorantar masu ziyara ya haura sama da shekaru 200 a duniya, kuma galibi masu ziyara kan sanya ruwa a cikinsa daga bisani su sha su kuma bada sadaka ga masu kula da shi domin neman tubarakki.

Ziyarar da galibin al’ummar Musulmi ke yi a Hubbaren na tallafa wa kasuwancin jama’a da dama, a cewar Murtala Abubakar ST wani haifaffen ɗan unguwar, “na shafe sama da shekaru 40 kuma anan aka haifeni, kasuwanci na bunqasa a duk lokacin da masu ziyara suka zo na al’ummar da ke wajen, kuma wannan ba ƙaramin tasiri ne da shi ba ga mu mazauna yankunan da ke zagaye da hubbaren nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *