Hukumar Ƙidaya ta fara aika gayyatar horarwa ga ma’aikatanta

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC) ta fara aika saƙon gayyata zuwa ga masu ƙidayar jama’a da masu sa ido don horar da ma’aikatan wucin gadi.

Sanarwar hukumar ta ce, “muna farin cikin sanar da duk waɗanda suka yi rajista a manhajar NPC domin gudanar da aikin ƙidayar jama’a na shekarar 2023 cewa, hukumar gudanarwar hukumar ƙidaya ta ƙasa ta fara aikewa da takardar gayyata horo ga ma’aikata da aka amince da su domin horar da matakin ƙaramar hukumar, wanda aka tsara zai fara a ranar 11 ga Afrilu, 2023.”

Dangane da saƙon da aka aika a gayyatar, NPC ta bayyana cewa za a gudanar da matakin farko na horar da ma’aikata daga ranar 11 zuwa 17 ga Afrilu 2023.

Gayyatar ta kuma ƙunshi cibiyoyin horar da masu ƙidaya da masu kula da masu halartar ƙaramar hukumar tasu.