Hukumar Abuja ta yi alƙawarin kaurara tallafinta ga tsofaffin sojojin Nijeriya

Daga AISHA ASAS

Hukumar Birnin Tarayya Abuja ta yi alƙawarin mara wa bikin Ranar Tunawa da Sojoji na 2022 baya don tabbatar da bikin ya cimma nasara.

Ministan Abuja, Malam Muhammad Musa Bello ne ya yi wannan alƙawari a lokacin da ya karɓi baƙuncin ƙungiyar tsofoffin sojojin Nijeriya a ofishinsa, tare da bada tabbacin FCTA za ta kaurara gudunmawarta don inganta walwalar tsofoffin sojoji da matan sojojin da suka rasa rayukansu a matsayin nuna godiya ga sadaukarwar da dakarun suka yi wa ƙasa.

Sanarwar da sakataren labarai na FCTA, Anthony Ogunleye ya sa wa hannu, ta nuna akwai kyakkyawar alaƙa tsakanin FCTA da tsofoffin sojoji. An kuma maƙala wa Ministan tambarin bikin Ranar Tunawa da Sojojin.

Ministan ya ce FCTA ta yi aiki tare da tsofoffin sojojin na tsawon shekaru inda takan ɗauki mambobinsu suna taimaka mata musamman a fannin tsaro da tattara bayanan sirri.

Tun farko da yake jawabi, jagoran tawagar kuma shugaban ƙungiyar tsofoffin sojojin, Major General Abdulmalik Jubril (rtd), ya ce Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ɗora musu alhakin su zaga su nemi haɗin kan da taimakon ‘yan Nijeriya masu kishin ƙasa don ci gaba da raya sadaukarwar da dakarun suka yi wa ƙasa yayin da suke bakin aiki.

Ya ƙarasa da cewa, “Shugaba Buhari ne uban ƙungiyarmu, kuma ya umurce mu da mu bi ‘yan Nijeriya, ministoci da ma’aikatu da sauran masu faɗa a ji a gwamnati don neman haɗin kansu kan harkokinmu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *