Hukumar Alhazai ta Jigawa ta maida wa maniyyata 609 da kuɗaɗensu

Hukumar Alhazai ta Jihar Jigawa ta maida wa maniyyata 609 waɗanda suka biya kuɗaɗe don Hajjin 2020/2921 da kuɗaɗensu har Naira miliyan 752.

Sakataren hukumar, Alhaji Muhammad Sani Alhassan, shi ne ya bayyana haka a Asabar da ta gabata yayin zantawarsu da manema labarai a garin Dutse, babban birnin jihar.

Alhassan ya ce, Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON), ita ce ta ba da umarnin da a gaggauta maida wa maniyyatan da kuɗaɗensu bayan da ƙasar Saudiyya ta bayar da sanarwar hana maniyyatan wasu ƙasashen duniya zuwa aikin Hajji a matsayin wani mataki na yaƙi da yaɗuwar cutar korona.

Alhassan ya bayyana cewa maniyyata 1,165 suka biya kuɗaɗensu don Hajjin 2020/2021.

Ya ce, “Daga cikin maniyyata 1,165, an maida wa mutum 609 da kudaɗensu yayin da maniyyata 556 suka zaɓi a ci gaba da riƙe nasu kuɗin don Hajji mai zuwa.”

Haka nan, ya ce yayin shirye-shiryen aikin Hajji na gaba za a ba da fifiko ga maniyyata 556 da ba su karɓi kuɗaɗensu ba.

A ƙarshe, Alhassan ya yi kira ga jama’a da su ci gaba da yin addu’ar zaman lafiya da samun daidaito ga ƙasa da kuma fatan ganin karshen annobar korona.