Hukumar alhazan Kebbi za ta rufe karɓar kuɗin maniyyata 5 ga Fabrairu

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi

Hukumar kula da jin daɗin Alhazai ta Jihar Kebbi ta sanar da rufe karɓar kuɗi daga hannun maniyyata aikin Hajjin 2025 daga ranar 5 ga Fabrairu, 2025.

Wannan yana ƙunshe ne a sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban hukumar Alhaji Faruk Musa Yaro ranar Talatar da ta gabata.

Takardar ta bayyana cewa wannan ya biyo bayan wani umarni ne daga hukumar jin dadin Alhazai ta ƙasa (NAHCON) bisa ga canje-canje da aka samu a cikin shirin aikin Hajjin bana.

Yanzu haka dai kawo yanzu hukumar ta jihar Kebbi ta kammala aƙalla kashi sittin cikin ɗari na biyan kuɗin maniyyata tun bayan da ta soma tattara kuɗaɗen maniyyata daga watan Satumbar shekarar da ta gabata ta 2024, saboda haka abinda ya rage kashi arba’in. Saboda haka a ke kira ga maniyyata da suka soma biyan kuɗin da su yi ƙoƙari su cika sauran abinda ya rage, su kuma waɗanda ke iya lokaci ɗaya da su biya tun kafin sabon wa’adin da hukumar ta diɓa ya cika.

Shugaban hukumar ya ƙara da cewa wannan hukumar ta ƙayyade naira milliyan takwas da dubu ɗari huɗu ne za a biya aƙalla kuma ana iya biyan kuɗin ta kowane banki ta yadda kuɗaɗen za su shiga asusun hukumar kafin a fitar da ainihin kuɗin da hukumar ta ƙasa za ta ƙayyade.

Ya kuma bayar da tabbacin adalci a wajen rabon kujerin aikin Hajjin inda ya ce duk wanda ya riga biya shi ne zai samu tukuna kafin waɗanda suka biya daga baya.

 Haka-zalika hukumar ta yi kira ga waɗanda suka biya kuɗin aikin Hajji a shekarar da ta gabata ta 2024 amma ba su samu zuwa ba kuma suka haƙura suka bar kuɗaɗensu a matsayin ajiya da su hanzarta cika abinda ya rage cikin lokaci.