Hukumar hada-hadar hannayen jari ta Nijeriya ta haramta hada-hadar kuɗaɗen intanet na Binance

Daga AMINA YUSUF ALI

Matakin na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da hukumar ta wallafa a shafinta na intanet.

Hukumar hada-hadar hannayen jari ta ƙasar ta ce kamfanin na Binance bai yi rajista da ita ba, a don haka ne ta ce ta haramta ayyukan kamfanin a faɗin ƙasar nan.

Sanarwar ta kuma gargaɗi ‘yan ƙasar da ke mu’alama da kamfanin da su dakata, in ba haka ba kuwa duk abinda ya same su to su kuka da kansu.

Sanarwar ta ci gaba da cewa ”An nusar da hukumar kula da hada-hadar hannayen jari ta Najeriya game da shafin intanet da kamfanin Binace ke gudanarwa, inda yake neman ‘yan Najeriya da su zuba jari kan harkar hada-hadar kuɗin intanet na Kirifto karansi a shafin nasa da wasu manhajojin wayar hannu.

Kan haka ne hukumar ce bayyana wa ‘yan ƙasar cewa ”kamfanin ‘Binance Nigeria Limited’ ba shi da rajista da hukuma, kuma baya aiki da dokokin hukumar kula da hannayen jari ta ƙasar, don haka duk abin da ya samu mutumin da ke mu’amala da kamfanin to ya kuka da kansa”.

Hukumar ta kuma shawarci ‘yan ƙasar da su guji zuba jari a harkar hada-hadar kuɗaɗen intanet ta Kirifto karansi a kamfanonin da ba su da rajista da hukumar.

Hukumar kula da hada-hadar hannayen jari ta Najeriyar ta buƙaci kamfanin ‘Binance Nigeria Limited’ da ya gaggauta dakatar da ayyukansa a faɗin ƙasar.

Hukumar ta kuma ce za ta bayyana matakan ladabtarwa da za ta ɗauka kan kamfanin da wasu takwarorinsa marasa rajista a ƙasar.

Ta qara da cewa, za ta yi aiki tare da hukumomin da lamarin ya shafa a ƙasar domin ɗaukar mataki game da batun.

A makon da ya gabata ne dai Hukumar kula da kasuwar hannayen jari ta Amurka ta shigar da ƙarar kamfanin na Binance a gaban kotu.

A ranar Alhamis ne kuma kamfanin ya ce ya dakatar da hada-hada da kuɗin dala na Amurka bayan matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka a kansa.

Wannna mataki dai ka iya kawo cikas ga kasuwar hada-hadar kuɗi ta intanet wato kirifto a Nijeriya, musamman ganin cewa a baya-bayan hukumar kula da kasuwar hannayen jari ta ƙasar ta haramta ayyukan kamfanin Paxful.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *