Hukumar Jami’ar Bayero ta yi ƙarin hutu ga ɗalibanta

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Hukumar Jami’ar Bayero ta Kano, ta sanar da yin ƙarin wa’adin komawar ɗalibai zangon karatu na 2021 da 2022.

Ƙarin hutun na cikin wata sanarwar da jami’in yaɗa labaran jami’ar, Lamara Garba Azare, ya fitar mai ɗauke da sa hannun maga-takardan jami’ar, Malam Jamilu Ahmad Salim.

Sanarwar ta ce, an cimma wannan matsaya ne a zaman majalisar zartaswar jami’ar karo na 392 da aka gudanar a Larabar da ta gabata.

A baya dai jami’ar ta sanya ranar 4 ga watan Oktoban 2021 a matsayin ranar komawar ɗaliban, sai dai yanzu an mayar da komawar ɗaliban zuwa ranar 1 ga watan Nuwamban bana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *