Daga JAMEEL GULMA a Kebbi
Hukumar jin daɗin Alhazzai ta jihar Kebbi ta bayyana ƙudurinta na soma hidima da jigilar masu zuwa aikin Umarah daga kowane ɓangaren ƙasar nan.
Shugaban hukumar na jihar Kebbi, Alhaji Musa Yaro Enabo ne ya bayyana haka ranar Larabar da ta gabata yayin da ya ke zantawa da manema labarai a ofishinsa da ke garin Birnin Kebbi.
Ya bayyana cewa yanzu haka dai hukumar ta bullo wani irin sabon shiri na soma jigila tare da hidima ga maniyyata aikin Umrah daga kowane ɓangare a Nijeriya.Ya bayyana cewa wannan ne karon farko da za’a fara jigilar maniyyata aikin Umrah daga jihar Kebbi kaitsaye tun kama daga masu zuwa Umrah ta kowane lokaci da kuma masu zuwa na musamman lokacin watan Ramadan sai dai kudin ne ya bambanta.
Alhaji Faruk Enabo ya kuma tabbatarwa maniyyatan akwai tanadi na musamman da hukumar ta yi a ɓangaren masauki, jigila da kuma kulawa da su yadda yadda ya kamata.
Ya kuma buƙaci maniyyata aikin Umrah da su biya kuɗinsu daga ranar 30-10-2024 har zuwa 30-11-2024. Inda yake bayarda tabbacin duk wanda ya biya kuɗin da aka tsara zai yi aikin shi na Umrah ba tareda saɓawa ba.
Faruk Enabo ya yabawa gwamantin maigirma Gwamna Malam Nasir Idris bisaga irin ƙwaringwiwa da ta ke bayarwa a duk lokacin da wani abu na cigaba ya zo musamman kan lamurran da suka shafi addini.