Hukumar Kiwon Lafiya ta Bauchi ta tabbatar da ɓullar cutar Ƙyandar Biri

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Shugaban hukumar kiwon lafiya a Matakin Farko ta jihar Bauchi, Dokta Rilwanu Mohammed ya tabbatar da ɓullar cutar Ƙyandar Biri, wato Monkey Pox a cikin jihar.

Dokta Rilwanu Mohammed ya shaida wa manema labarai a kwanakin baya cewar, bayan tabbatar da cutar ga wani mutum, ana kuma gwajin wasu mutane biyu da ake ganin sun kamu da ita wannan cuta.

“Harbabbe daga cutar ya fito daga Jihar Adamawa ne, kuma a halin yanzu ana yi masa tattalin kiwon lafiya daga wannan cuta a wata keɓaɓɓiyar cibiyar kiwon lafiya dake cikin jihar ta Bauchi. Ba za mu sake shi ya tafi ba har sai mun tabbatar da ingancin lafiyar sa, saboda kada ya harbi wasu mutune dabam”, inji Dokta Mohammed.

Shugaban hukumar ta kiwon lafiya sai ya bayyana cewar, “ba kamar cutar Kwalara ba, wanda mutum zai jira kamuwar cuta kamar guda 15 kafin mutum ya aiyana ɓarkewar, za’a iya aiyana ɓarkewar wannan cuta ta Ƙyandar Biri koda da kamuwar mutum ɗaya ne.

Dokta Rilwanu amma ya tabbatar wa jama’a cewar, hukumar sa da haɗin kan abokan jera tafiya, tana matuƙar ƙoƙarin daƙile bazuwar wannan cuta zuwa wasu sassan jiha.

Rilwanu ya kuma bayyana cewar, an ƙarfafa bin ba’asi domin tabbatar da samun lafiyar wanda ya kamu da cutar ta Ƙyandar Biri, sai ya buƙaci jama’a da su lura da alamomin cutar domin gujewa kamuwa.

Ya zayyana alamomin cutar da suka haɗa da zazzaɓi, ciwon kai, gaɓoɓi da baya, ƙananan kumburi a fatar jiki kamar ƙuraje, jin sanyi da gajiya tiƙis, ƙurajen baki, da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *