Daga AMINA YUSUF ALI
Babban Bankin Nijeriya, CBN ya gabatar da wani sabon tsarin da zai hana hukumar Kwastan cajar masu shigowa ko fita da kaya a ciki da wajen Nijeriya ba bisa ƙa’ida ba.
CBN ɗin ya ƙaddamar da sabon tsarinsa na ‘evaluator’ da ‘e-Invoice’ waɗanda da su ne tsari na yanar gizo da ‘yan kasuwa za su dinga amfani da su don biyan kuɗin shige da fice da kaya ba tare da an yi musu lissafin awon igiya kamar yadda yake faruwa a baya.
Wannan bayani dai ya fito ne daga wata sanarwa da Babban Bankin ya wallafa mai ɗauke da sa hannun Dakta. O. S. Nnaji, Daraktan sashensu na kasuwanci. Takardar na ɗauke da taken: ‘dokokin amfani da e-‘evaluator’ da ‘e-Invoice’. Inda aka bayyana cewa, takardar an yi ta ne don sanarwa ga dukkan diloli da ‘yan kasuwa da kuma sauran al’umma.
Gwamnan CBN ya bayyana cewa, wannan tsari shi zai sa a samu lissafi mara kuskure a kan ƙididdigar kuɗaɗen da ake biya domin shige da ficen safarar kaya a Nijeriya. Sannan a kauce wa aringizon lissafi.