Hukumar Kwastam ta tara bilyan N4b a cikin wata guda

Daga FATUHU MUSTAPHA

Hukumar Yaƙi da Fasa Ƙwauri ta Ƙasa reshen Oyo/Osun ƙarƙashin jagorancin Comptroller AR Abdulkadir, ta ce ta samu nasarori da daman gaske wajen aiwatar da harkokinta.

Yayin ganawar da ya yi da manema larabai a Alhamis da ta gabata, Comptroller Abdulkadir ya ce a watan Janairun da ya gabata kaɗai sun tara wa gwamnati kuɗin shiga da ya kai sama da bilyan N4.895.

Ya ce tsakanin Nuwamba da Janairun da suka gabata, sun yi nasar kama ɓatagari da dama da kuma kayayyakin fasa ƙwauri wanda a kiyasce harajinsu ya haura Naira milyan 393.

A cewar jami’in, kayayyakin da suka kama sun haɗa da; tabar wiwi mai nauyin kilogram 20, da shinkafar ƙetare buhu 3,052 da jarkokin man girki da dama da gwanjon sutura da tayoyin mota 246 da mota kirar Toyota Camry guda 8, da babura guda 10 waɗanda ake amfani da su wajen shigo da shinkafa ta ɓarauniyar hanya, da dai sauransu.

Abdulkadir ya yaba da irin gundumawar da takwarorinsu a yankin kan ba su wajen gudanar da ayyukansu.

Haka nan, ya yaba da haɗin kan da suke samu a wajen sarakunan gargajiya da masu faɗa a ji da ma al’umma baki ɗaya a Oyo da Osun.

Ya ƙarasa da cewa yaƙi da harkokin fasa ƙwauri abu ne da hukumarsu za ta ci gaba da yi domin ƙarfafa tattalin arzkin ƙasa da kuma tsaftace al’umma daga miyagun ƙwayoyi.