
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Hana Safarar Ɗan-adam (NAPTIP), ta dakatar da wani Mista Akwaowo Jonah Emmanuel bisa zargin karya dokar aikata masha’a da cin zarafin mata masu laifi.
NAPTIP ta dakatar da Emmanuel ne, wanda shi ne Shugaban jami’an Sufuri na ofishinta dake Uyo a Jihar Akwa-Ibom, wanda kuma ake zargin sa da cin zarafin marasa galihu da aka ajiye a ƙarƙarshin kulawarsu har zuwa lokacin da za a kammala bincike.
Rahotonni sun bayyana cewa, ya kan faɗa wa mai laifi cewa za ta samu ƴancin ficewa daga hannunsu matuƙar ta amince da buƙatarsa.
NAPTIP ta ce hakan ya biyo bayan rahoton da ƙwarya-ƙwaryar kwamitin bincike game da lamarin ya fitar ne kan zargin da ake yi wa jami’in.
Rahoton kwamitin manyan jami’ai shi zai bada bayani game da matsayar hukumar akan jami’in.