Hukumar NDLEA ta cafke mace mai goyo, mai juna-biyu, da wasu 26 da muggan ƙwayoyi

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Hukumar yaƙi da sha, da fatauci da miyagun ƙwayoyi ta NDLEA ta bayyana cewar, ta yi nasarar cafke mutane 28, cikin su har da mace mai juna biyu, da wata mai goyo, haɗi da wani ɗalibin jami’a ɗan aji biyu a makaranta da buhunan tabar wiwi waɗanda aka ƙiyasta nauyin su akan kilogiram dubu tara da ɗari huɗu da talatin da bakwai, da ɗigo shida haɗi da ƙwayoyi opioids guda 138, 053, da ma wasu ƙwayoyin daban-daban.

A cikin wani jawabi da ya fitar a ranar Lahdi da ta gabata, mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya ce cafke miyagun ƙwayoyin da tsare masu laifukan ya gudana ne cikin wani shantali da jami’an hukumar suka gudanar a tsakanin jihohin Yobe, Ondo, Edo, Ribas, Akwa Ibom, Imo, Jigawa, Kogi, Adamawa, Kaduna, Kwara, Legas da birnin tarayya ta Abuja, a ‘yan kwanakin nan Babafemi ya bayyana cewar, ɗalibin yana karatun sadarwa ne a Jami’ar NOUN ta Nijeriya; sai Mis Mercy Nyong mai shekaru 30 da haihuwa da aka cafke ta a ranar Laraba 12 ga watan Oktoba, 2022 a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Mohammed dake Legas yayin da take ƙoƙarin ficewa waje zuwa Ƙasar Dubai, a ƙunshe a cikin kwalayen turaren wuta.

Jawabin ya ƙara da cewar, dakarun na NDLEA a ranar sati ne dagata 15 ga wannan wata na Oktoba suka yi tsinke wa wani ƙauye mai suna Chukuku, kimanin tafiyar kilomita 10 daga Gwagwalada, inda suka bankaɗo wani gidan ajiyar tabar wiwi.

“Manyan buhunan bagco guda 510 na kayan maye aka iske shaƙe a gidan masu nauyin jimlar kilogiram 5, 640 a wani tafkeken ɗaki, tare da wata mace mai goyo, mai suna Sa’adatu Abdullahi ‘yar shekara 35 da haihuwa, wacce take lura da gidan”.

Jawabin ya kuma bayyana cewar, an cafke kilogiram 48 na tabar wiwi a garin Buni Yadi na jihar Yobe; da kilogiram 31 da aka kame a garin Potiskum a hannayen wasu mutane biyu, Mohammed Mamuda da wata matar aure mai juna biyu dake da suna Hauwa Haruna.

A kuma yankin Ogbese na jihar Ondo, an cafke buhunan tabar wiwi guda 99 da wasu buhuna uku na irin shukawa na tabar waɗanda a jimlace nauyin su ya kai kilogiram 1,286; yayin da jihar Edo aka cafke kilogiram 410 na tabar wiwi, haɗi da babur na hawa da bindigogi ƙirar hannu guda biyu, aka kuma cafke masu laifukan guda biyu, Numga Anim mai shekaru 30 da Friday Ebije mai shekaru 50.

“Kazalika a ƙauyen Ekpom dake ƙaramar hukumar Igueben na jihar Edo an datse buhunan tabar wiwi guda 50 masu nauyin kilogiram 623 a hannun mai laifin Lucky Henry ɗan shekara 30; yayin da aka cafke wani mai laifin Ndidi Esegine mai shekaru 52 a cikin dajin Ugbodo na ƙaramar hukumar Ovia Arewa maso Gabas da kilogiram 266 na tabar wiwi a ranar Talata 11 ga watan Oktoba,” inji sanarwar.