Hukumar NDLEA ta cafke ‘yan zaman sheƙe aya 84 a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, NDLEA, shiyyar Kano, ta cafke mutane 84 yayin samamen da ta kai wani wurin shaƙatawa mai suna Bubble Club.

Hukumar, ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, ASN Sadik Muhammad Maigatari, ya fitar ranar Talata.

ASN Sadik ya ce, sun samu ƙorafe-ƙorafe daga mazauna yankin cewa suna zargin an mayar da wurin na shaye-shayen miyagun ƙwayoyi wanda hakan ya sa Kwamandan hukumar Abubakar Idris, ya fara tura jami’an hukumar na farin kaya domin tabbatar da zargin, kuma daga bisani ya bada umarnin tura dakarun hukumar cikin shirin ko-ta-kwana tare da killace wurin baki ɗaya.

Ya ƙara da cewa, bayan kai samamen da hukumar ta kai ta samu nasarar kama maza 55 da kuma mata 30 a yayin da wasu suka yi ƙoƙarin haura katanga wasu kuma suka yi yunƙurin ɓuya a cikin na’urar sanyaya ruwan sha, amma daga bisani jami’an hukumar sun cafke su.

Kazalika, sanarwar ta cigaba da cewa, hukumar NDLEA ba za ta saurara ba wajen ganin ta kawo ƙarshen duk wasu dilolin ƙwayoyi da kuma masu shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a ɗaukacin Jihar Kano.