Hukumar NEMA ta raba tallafin kayan abinci na Sarkin Saudiyya ga ‘yan gudun hijirar Borno

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA, ta fara rabon kayayyakin abinci da cibiyar bada agaji ta Sarki Salman, KSrelief, ta raba wa sansanonin ‘yan gudun hijira guda takwas da kuma al’ummar jihar Borno.

A cewar wata sanarwa a ranar Larabar da ta gabata ta bakin shugaban sashen yaɗa labarai na NEMA, Manzo Ezekiel, Gwamna Babagana Zulum ne ya ƙaddamar da rabon abincin a sansanin ‘yan gudun hijira na El-Miskin dake Maiduguri tare da taimakon babban daraktan hukumar ta NEMA, Mustapha Habib-Ahmed.

A nasa jawabin, Gwamna Zulum ya miƙa godiyarsa ga Sarkin Saudiyya Salman bin Abdulaziz Al Saud bisa tallafin da Cibiyar Bayar da Agajin Gaggawa ta Sarki Salman da Hukumar NEMA ta taimaka wajen kai kayan agaji da rarraba wa ‘yan gudun hijirar.

Gwamnan wanda ya bayyana cewa tallafin ya zo kan lokaci, ya kuma bada tabbacin cewa za a raba kayayyakin cikin adalci a sansanonin da aka gano.

Yayin da yake gargaɗin jami’an jihar da suka da su shiga wani hali, Zulum ya bayyana cewa, “ba za mu bari a karkatar da wannan tallafi a ƙarƙashin kulawa ta ba.”

Shi ma da yake jawabi, babban daraktan hukumar ta NEMA, ya bayyana cewa an bada tallafin ne domin ciyar da gidaje 16,000.

Shugaban ya ce kowanne daga cikin gidajen zai samu jimillar kwandon abinci mai nauyin kilogiram 59.8 wanda ya ƙunshi kilogiram 25 na shinkafa; kilo 25 na wake; kilo 4 na Masara Vita gari; kilo 2 na tumatir; lita 2 na man gyaɗa; kilo 1 na gishiri da kilo 0.8 na dunƙulen maggi.

“Kayayyakin tallafin an yi su ne domin tallafa wa ‘yan Nijeriya da ke fama da tashe-tashen hankula da kuma waɗanda bala’in ambaliyar ruwa ya shafa a jihar Borno a shekarar 2022,” inji shi.

Ya ce Masarautar Saudiyya ta bayar da tallafin ta tabbatar da cewa ta kasance aminan Nijeriya nagari saboda tausayawa ‘yan Nijeriya a lokacin da ake cikin mawuyacin hali.

Ya ce, kwandunan abinci 16,000 na daga cikin tallafin da aka bayar na ciyar da gidaje 16,000 a Borno. Sauran sun haɗa da kayan gini, buƙatun gida, kayan abinci da sauransu.