Hukumar NFC ta naɗa Shugaban MOPPAN, Dr. Sarari, jagoran kwamitin bajekolin finafinai na ƙasa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

An naɗa Shugaban Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinan Hausa ta Nijeriya (MOPPAN), Dr. Ahmad Muhammad Sarari, a matsayin Shugaban Ƙaramin Kwamitin Shirya Bajekoli na Ƙasa (Zuma Film Festival) na bana, wato shekara ta 2022, mai kula da Shiyyar Kano da Kaduna a bajekolin da zai gudana a ranakun 2 zuwa 8 ga Afrilu, 2022.

Naɗin na ƙunshe ne a cikin wata wasiƙa da Daraktan Shirin Bajelkolin, Edmund Peters, ya aike wa Shugaban na MOPPAN mai ɗauke da kwanan watan 15 ga Fabrairu, 2022, kuma Blueprint Manhaja ta samu kwafi.

A cikin wasiƙar, hukumar da ta ke shirya bajelokin, wato Hukumar Shirya Finafinai ta Nijeriya (NFC), ta buƙaci Dr. Sarari ya shirya tsaf tare ninka ƙoƙarinsa da masu ruwa da tsaki, don kula da ayyukan bajekolin wannan shekara a yankin Kano zuwa Kaduna.

Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da: Tsohuwar Shugabar MOPPAN reshen Jihar Kaduna kuma Sakatariyar Kuɗi ta Ƙungiyar MOPPAN ta Ƙasa, sannan Shugabar Ƙungiyar Matan Kannywood ta Ƙasa (K-WAN), Hajiya Fatima Ibrahim Lamaj, da kuma Shugaban Riqon Ƙwarya na ƙungiyar MOPPAN Reshen Jihar Kano kuma Mataimakin Babban Sakataren MOPPAN na Ƙasa, Jarumi Umar Gombe. 

Da ƙarshe kuma Hukumar ta NFC ta nuna matuƙar farin cikinta da naɗin da ta yi wa Shugaban MOPPAN ɗin na ƙasa, Dr. Ahmad Sarari, da sauran mambobin kwamitin bakiɗaya tare yi musu fatan sauke nauyin da aka ɗora musu lafiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *