Hukumar Shari’a ta ƙaddamar da kwamitocin sauye-sauye na cigaban shari’a a Kano

Daga RABIU SANUSI a Kano

Hukumar Shari’a ta jihar Kano ƙarƙashin jagorancin muƙaddashin shugabanta, Sheikh Malam Ali ɗan Abba, ta ƙaddamar da kamitocin da za su ɗauki gabarar kawo sauyi a jihar Kano kan abinda ya shafi shari’ar Musulunci, ranar Laraba.

Manyan baƙin da suka samu damar zuwa sun haɗa da Barista Mujiburrahman, tsohon shugaban ƙungiyar lauyoyi ta jihar reshen Ungoggo kuma tsohon shugaban ƙungiyar lauyoyi Musulmi ta Kano; sai Baba Jibo Ibrahim mai, magana da yawun kotuna ta jihar Kano; wakilin shugaban gidajen gyaran hali da tarbiyya ta Kano; wakilin kwamishinan ‘yan sandan jahar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa da sauran mambobi na hukumar da manyan limamai.

Ya ce, babban ƙalubalen da za su fara da shi shine sulhu kamar yadda shugaba sallahu Alaihi Wasallama ya yi, sannan iyaye su saka ‘ya’yan su a gaba wajen tsaida sallah, domin tsaida sallah shine babban jigon magancewar waɗannan matsalolin da aka ciki a jihar na shaye-shaye, kwacen waya, tabarbarewar tarbiyya raba da yawan cinkoso a gidajen gyaran hali, matsalolin aure da sauran matsaloli da ake fuskanta, inda ya tabbatar da faɗin Allah na cewar tsaida sallah na hana alfasha da sauran miyagun ayyuka. 

Waɗannan kwamitoci da aka samar sun haɗa da;

Da’awa; Sulhu; Tantance limamai da ladanai; Bita da wayar da kan al’umma kan addini.

“Da fatan za su kawo cigaba da haɗin kan al’ummar jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya,” kamar yadda Maifirma Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf yake masu fata.

A ƙarshe ya yi kira ga al’umma da iyaye wajen bada haɗin kai da goyon baya wajen warware kowacce irin matsala cikin sauƙi.

A nasa ɓangaren shugaban ƙungiyar lauyoyi ta jihar Kano Barista Mujiburrahman ya ce ya ji daɗin wannan gayyata da aka masa, kuma a saninsa tun daga lokacin Malam Ibrahim Shekarau ba a taɓa wata gwamnati a jihar nan da take ƙoƙarin haɓaka Shari’a ba sai wannan gwamnatin ba.

Ya ce, a baya sun yi irin wannan ƙoƙarin kafa kwamitin Sulhu a ƙananan hukumomi wanda an yi ayyukan sulhu kala-kala wanda da Allah yasa an cigaba da wannan tsarin da Kano ta wuce haka.

Ya kuma yi kira ga gwamnan Kano kan inganta hukuma ta Shari’a kamar yadda ta ke a baya da sauran hukumomin addini na Kano.

Ga sunayen ‘yan kwamitin kamar haka: 

Kwamatin sulhu: Wanda Ibrahim Inuwa (Limamin Ja’en) zai kasance a matsayin Shugaba da Ibrahim Lawan ƙaraye DPRS a mataimakin shugaba; Aliyu Umar Kibiya (Limamin Kibiya) Mamba; Nana Aisha Muhammad ACEO a matsayin Mamba; da Abubakar I. Sulaiman PEO a matsayin Sakatare.

Sai Kwamitin Da’awa, wanda Kabiru Na’ibi ƙaraye zai kasance a matsayin Shugaba; Muhammad Abu Musa DIP a matsayin mataimaki da Nasiru Aliyu Harazimi, Abubakar Sani, Yawale Sulaiman Gulu, Zainab Sani Matori a matsayin mambobi. Sai kuma Hamisu Murtala Gwarzo a matsayin Sakatare.

Kwamatin Tantance Limamai da Ladanai ya haɗa da Muh’d Mukhtar Mama Darma, wanda shi zai kasance a matsayin shugaba; Yusha’u Abdullahi Bichi DIE a matsayin mataimaki da Muhammad Abu Musa DIP, Naziru Saminu ɗorayi da Adamu Ibrahim a matsayin mambobi, sai Adnan Nasir Koki a matsayin sakatare.                                       

Kwamitin Bita da Wayar da Kan Al’umma kan Addini yana da Malam Abubabakar Sharif Bala a matsayin shugaba da Sani Zarewa DSD a matsayin mataimaki da Mahbub Sarki DISA, Abdullahi Hassan, Balarabe Aliyu da Maryam Lawan a matsayin mambobi. Sai kuma Sani Musa Muhammad a matsayin sakatare.