Hukumar shari’a ta Jigawa ta kori jami’ai 3 da shawartar alƙalai 2 su yi murabus

Daga BELLO A. BABAJI

A ƙoƙarinta na daƙile rashawa da ke cikin harkokin shari’a a Jigawa, Hukumar kula da Harkokin Shari’a ta jihar, ta fara ɗaukar mataki akan jami’an ɓangaren a jihar.

A cikin wata takarda da Sakataren hukumar, Barista Auwalu Ɗan’azumi ya fitar, hukumar ta karɓi rahoton kwamitin bincike daga babbar kotu game da wani jami’i mai suna Iyal Ibrahim da Baffa Alhaji waɗanda aka samu da laifin sayar da wasu motocin Babbar Kotun Tarayya da ke Dutse.

An yanke wa mutane biyun hukuncin kora daga aiki ƙarƙashin dokar hukumar shari’ar sashe na 41 da kuma ta jihar sashe na 20.

Sanarwar ta ce hukumar ta kuma karɓi rahoton jami’i Abdu Hassan Aujara kan karɓar kafin-alƙalami na Naira 965,000 a wani batu da bankin Ja’iz ya gabatar wa Kotun Shari’a ta Jahun wanda akan hakan shi ma aka sallame shi a aiki.

Haka nan hukumar ta yi hukunci game da wani rahoto da kwamitin sauraron koken shari’a (IPCC) ta kai mata na Alƙali Adamu Isiyaku Farin Dutse wanda ya aka zarge shi da cin mutuncin shari’a da kuma saɓa ma ta, wanda aka gargaɗe shi a lokuta da dama. Don haka ne hukumar ta nemi da ya ajiye aikinsa.

Sannan hukumar ta yi nazari game da rahoton IPCC akan wani Alƙali Usman Usman Zubair, wanda Alƙalin wata kotun shari’a ne da aka zarge shi da rashin martaba ikon shari’a da kuma raba gado da wanda bai cancanci a ba shi wani kaso ba. Bayan gargaɗi da dama da aka yi masa ne, sai hukumar ta nemi da ya yi murabus.

Bugu da ƙari, hukumar ta aika da saƙon gargaɗi ga wani Alƙalin Kotun Shari’a na Gumel mai suna Munnir Sarki Abdullahi bisa juya shari’ar al’umma ta zama ta manyan laifuka tare da sanya kansa acikin ta.