Hukumar Shari’ah ta ƙaddamar da kwamatocin sauye-sauye na cigaban shari’a a Kano

Daga BELLO A. BABAJI

Hukumar Shari’ah ta jihar Kano ƙarƙashin jagorancin muƙaddashin shugabanta, Sheikh Malam Ali Ɗan Abba, ta ƙaddamar da kamitocin da za su ɗauki gabarar kawo sauyi a jihar Kano kan abinda ya shafi shari’ar Musulunci, ranar Laraba.

Manyan baƙin da suka samu damar zuwa sun haɗa da Barista Mujiburrahman, tsohon shugaban ƙungiyar lauyoyi ta jihar reshen Ungoggo kuma tsohon shugaban ƙungiyar lauyoyi Musulmi ta Kano; sai Baba Jibo Ibrahim mai, magana da yawun kotuna ta jihar Kano; wakilin shugaban gidajen gyaran hali da tarbiyya ta Kano; wakilin kwamishinan ƴan sandan jahar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa da sauran mambobi na hukumar da manyan limamai.

Ya ce, babban ƙalubalen da za su fara da shi shine sulhu kamar yadda shugaba sallahu Alaihi Wasallama yayi, sannan iyaye su saka ya’yan su a gaba wajen tsaida sallah, domin tsaida sallah shine babban jigon magancewar waɗannan matsalolin da aka ciki a jihar na shaye-shaye, kwacen waya, tabarbarewar tarbiyya raba da yawan cinkoso a gidajen gyaran hali, matsalolin aure da sauran matsaloli da ake fuskanta, inda ya tabbatar da faɗin Allah na cewar tsaida sallah na hana alfasha da sauran miyagun ayyuka.

Hakazalika, ya yi kira ga limamai da ladanai kan samun haɗin kai idan dai Allah aka nufata, a ƙarshe yayi fatan

Waɗannan kwamitoci da aka samar sun haɗa da;

-Da’awa
-Sulhu
-Tantance limamai da ladanai
-Bita da wayar da kan al’umma kan addini

Da fatan za su kawo cigaba da haɗin kan al’ummar jihar Kano da ma kasa baki ɗaya, kamar yadda mai girma Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ke masu fata.

A karshe ya yi kira ga al’umma da Iyaye wajen bada haɗin kai da goyon baya wajen warware kowacce irin matsala cikin sauƙi.

A nasa bangaren shugaban kungiyar lauyoyi ta jihar Kano Barasta Mujiburrahman yace yaji dadin wannan gayyata da aka masa, kuma a saninsa tun daga lokacin Malam Ibrahim Shekarau ba a taba wata gwamnati a jihar nan da take kokarin habaka Shari’a ba sai wannan gwamnatin ba.

Ya ce, a baya sun yi irin wannan ƙoƙarin kafa kwamitin Sulhu a ƙananan hukumomi wanda an yi ayyukan sulhu kala-kala wanda da Allah yasa an cigaba da wannan tsarin da Kano ta wuce haka.

Ya kuma yi kira ga gwamnan Kano kan inganta hukuma ta Shari’a kamar yadda ta ke a baya da sauran hukumomin addini na Kano.

Ga sunayen ƴan kwamatin kamar haka

Kwamatin sulhu

1.Ibrahim Inuwa (Limamin Ja’en) Ciyaman

  1. Ibrahim Lawan Ƙaraye DPRS mataimakin ciyaman
  2. Aliyu Umar Kibiya (Limamin Kibiya) Mamba
  3. Nana Aisha Muhammad ACEO Mamba
  4. Abubakar I. Sulaiman PEO Secretary

Kwamitin DA’AWA

  1. Kabiru Na’ibi Karaye (Board Member Chairman)
  2. Muhammad Abu Musa DIP mataimaki
  3. Nasiru Aliyu Harazimi Board Member Mamba
  4. Abubakar Sani Maɗatai Board Mamba

5.Yawale Sulaiman Gulu Mamba

  1. Zainab Sani Matori Mamba

7.Hamisu Murtala Gwarzo Sakatare

Kwamatin Tantance limamai da ladanai

  1. Muh’d Mukhtar Mama Darma Ciyaman
  2. Yusha’u Abdullahi Bichi DIE mataimaki
  3. Muhammad Abu Musa DIP Mamba
  4. Naziru Saminu Ɗorayi Board Member Mamba
  5. Adamu Ibrahim Mamba
  6. Adnan Nasir Koki Secretary

Kwamatin Bita da wayar da kan al’umma kan addini

1.Malam Abubabakar Sharif Bala Ciyaman

  1. Sani Zarewa DSD mataimaki
  2. Mahbub Sarki DISA Mamba
  3. Abdullahi Hassan Mamba
  4. Balarabe Aliyu Mamba

6.Maryam Lawan Mamba

  1. Sani Musa Muhammad Sakatare