Hukumar tace finafinai ta Jihar Kano ta ƙwace yin rajistar ‘yan fim daga ƙungiyoyi zuwa ofishinta

DAGA MUKHTAR YAKUBU

A yanzu haka dai hukumar tace finafinai ta Jihar Kano ta ƙwace tare da dawo da yin rajistar ‘yan fim daga hannun ƙungiyoyin ‘yan fim da ta damƙa musu a baya zuwa ofishinta domin ci gaba da yin rajistar ‘yan fim ɗin, tare da bayar da tsawon sati uku ga duk wanda bai yi rajistar ba, to ya zama wajibi ya je ofishin Hukumar tace finafinai ya yi rajistar domin kaucewa ɗaukar matakin da ya dace a kansa

Haka kuma hukumar ta bayar da umarnin hana daukar duk wani fim ( shooting) ko sakin sa ba tare da an tace shi ba wanda a cewar ta saba wannan umarnin ka iya saka mutum ya fuskaci fushin doka tare da yin da na sani.

Shugaban Hukumar tace finafinai ta Jihar Kano Abba El-mustapha ne ya sanar  da hakan a  ranar Litinin 10 ga Yuni 2024 a cikin jawabin sa ga manema labarai tare da jagororin ‘yan masana’antar Kannywood da suka haɗa da ‘Kannywood Foundation,’ ‘Arewa films Markers,’ ‘Artists Guilds of Nigeria ‘da kuma Ƙungiyar MOPPAN.

Abba El-Mustapha ya ƙara jaddada cewa ya zuwa wannan lokaci hukumar ta bai wa ‘yan masana’antar Kannywood wa’adin sati uku, wato daga ranar  10 ga Yunin 2024 zuwa 1 ga Yunin 2024 don kowa  ya  zo ya yi rijista kafin ‘yan kwamitin su fara aiki.

Kwamitin da za su yi aikin sun haɗa da wakilan ƙungiyoyin da aka yi wannan zaman da su da kuma ma’aikatan hukumar.

Don haka ga duk mai buƙatar yin rajista a yanzu zai je ofishin hukumar ne da ke kan titin Maiduguri a cikin garin Kano.

Tun a farkon zuwan sa hukumar ne Abba El-Mustapha a ƙoƙarin sa na kawo gyara tare da  tsaftace harkar fim ya kawo sabbin tsare-tsare, ciki har da sabunta rajista ga dukkan masu gudanar da sana’a a cikin masana’amtar finafinai ta Kannywood, wanda hakan ya jawo surutai tare da tayar da kayar baya ga wasu daga cikin ‘yan fim musamman ma waɗanda suke cikin gwamnatin irin su Sunusi Oscar 442 wanda shi ne babban mai ba gwamnan Kano shawara a kan harkar fim.

Bayan kai ruwa rana ne da aka samu a wancan lokacin bisa neman maslaha hukumar ta dawo da yin rajistar ‘yan fim ɗin zuwa hannun ƙungiyoyin ‘yan fim ɗin kamar yadda suka buƙata.

Sai dai tun daga lokacin da tsarin rajistar ya dawo hannun ƙungiyoyin ‘yan fim babu wani abu da aka samu na ci gaba da yin rajistar.

Wani bincike da muka gudanar a tsakanin ‘yan fim ɗin ya tabbar da cewar tun da aka fara yin rajistar zuwa yanzu  ‘yan fim kashi biyu ne daga cikin kashi 10 suka yi rajistar, kuma a cikin su har da mutane 50 da Abdul Amart ya biya wa rajistar.