Hukumar Tace Finafinai ta Nijeriya na son a riƙa shirya finafinan da za su janyo hankalin masu zuba jar

i

Daga BELLO A. BABAJI

Babban Daraktan Hukumar Tace Finafinai ta Nijeriya (NFVCB), Dakta Shua’ibu Husseini ya shawarci jagororin shirya finafinai a Nijeriya su ke samar da waɗanda za su ke janyo hankalin masu zuba hannun-jari don ci-gaban masana’antar.

Daraktan ya yi kiran ne a lokacin da ya ke gabatar da wani jawabi a taron ƙara wa juna sani da masana’antar Kannywood ta shirya a ranar Laraba, a Kano.

Ya ce, duk da cewa masana’antar fim a Nijeriya na samun ci-gaba, akwai buƙatar ake samar da finafinai masu ma’ana da za su taimaka wajen yin nasara a kasuwancin masana’antun finafinai.

Ya ƙara da cewa, ana da buƙatar samun nuna ƙwarewa yayin shirya fim ta yadda hakan zai taimaka wa bunƙasar masana’antar da ma kasuwancinta.

Har’ilayau, Dakta Husseini ya ce akwai masu shirya fim da dama da ba sa gabatar da finafinansu ga hukumar don ta yi nazari game da su wanda yin hakan ya saɓa wa doka kuma abun ne da ke haifar da koma baya ga harkar fim a Nijeriya.

Ya kuma ce, su na cigaba da ƙoƙari wajen ganin an tabbatar da masu shirya fim su na samun taimako na kayayyakin aiki da kuma kuɗi don haɓaka harkokinsu.