Hukumar tsaro ta damƙe mutum 4 da jabun sabon kuɗi na N1.9m

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Tsaron Farin Kaya (NSCDC) ta kama wasu mutum huɗu da suka ƙware wajen buga jabun kuɗaɗe.

Cikin sanarwar da ya fitar ranar Juma’a, Kakakin NSCDC, Kwamanda Olusola Odumosu, ya ce an damƙe waɗanda lamarin ya shafa ne a garin Jos, babban birnin Jihar Filato.

A cewar Odumosu sun kama tawagar farko da ta ƙunshi mutum huɗu da jabun kuɗi Dala 64,800 fa kuma Naira 475,000.

Yayin da suka kama tawaga ta biyu mai ƙunshe da mutum biyar ɗauke da jabun Naira miliyan 1.5.

Ya ce duka waɗanda aka kama ɗin ‘yan shekara tsakanin 24 zuwa 56.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *