Hukumar Yan Sanda ta kasa ta tuhumi shashin ta na kula da sharia

Babban Sufeton yan sanda na kasa, ya bada umarnin a tuhumi lauyan hukumar da kuma sashen sharia na hukumar yan sandan akan batun shigar da karar da hukumar ta yi, a gaban kotu, in da ta nemi kotu da ta hana jihohin kafa kwamitin binciken zanga-zangar
Endsars.

Mai magana da yawun hukumar yan sandan, mataimakin kwamishinan yan sanda Frank Mbah ne ya sanar da manema labarai, wannan mataki da hukumar ta dauka. Kakakin ya bayyana wa manema labarai cewa, tun ranar Alhamis da ta gabata, hukumar ta aika wa shugaban sashin takardar neman ya kare kansa ya bada  dalilan da za su hana a hukunta shi, akan shigar da wannan kara.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya, ya hakaito cewa, jihohi da dama sun kafa wannan kwamitin bincike a matakin jiha, domin ba wa mutane damar, gabatar da korafe-korafen su akan wannan hukuma da aka rushe ta SARS, tun bayan da zanga-zangar kin jinin hukumar ta lafa.

Bayanin da hukumar yan sandan ta fitar ya bayyana cewa “Babban sufeton yan sanda IGP M A Adamu, ya bada umarnin a binciki dalilin shigar da karar da akayi, akan hana jihohi kafa kwamitin bincike akan badakalar rusasshiyar hukumar nan ta SARS.

Mbah ya kara da cewa, Sufeton ya bada umarnin ne, tun bayan da kafafen watsa labarai suka fitar da wata sanarwa, a ran 3 ga watan Disamba, da ke cewa hukumar yan sandan  ta shigar da kara, akan kotu ta hana jihohi kafa wadannan kwamitoci. Wannan dalili ne ya sanya, sufeton ya bada umarnin a binciki sashin sharia na hukumar, umarnin da ya hada har da shugaban sashin”.

A saboda haka, hukumar take tuhumar sashin na sharia, kuma ba za ta yi kasa a guiwa ba, wurin ladabtar da duk wanda aka samu da sakaci da aiki ba, akan wannan matsala” in ji Mista Mbah.

Bayanin ya kara da cewa, babban sufeton yan sanda ya jaddada matsayin hukumar na sauke nauyin da aka daura mata, ta hanyar da doka ta tanada, da kuma nuna goyon bayanta ga rushe hukumar SARS da kafa kwamitocin bincike da jihohi su ka yi.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*