
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Katsina, ta shirya gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi a ranar asabar mai zuwa.
Kwamishinan zaɓe na jihar, Alhaji Lawal Faskari ya bayyana haka da ya ke hira da manema labarai a ofishinsa.
Ya ce tuni hukumar ta aika da kayan zaɓe zuwa ƙananan hukumomi 34 dake faɗin jihar.
Lawal Faskari ya ce a wannan karon kowacce ƙaramar hukuma tana da nata katin zaɓe da ya sha banban da na sauran.
Ya bayyana cewa hukumar da ɗauki ma’aikatan wucin-gadi guda dubu ashirin da aka ba su horo, inda kuma tuni aka tura su ƙananan hukumomin.
Kwamishinan ya sanar da cewa akwai rundunar zaɓi 361 da kuma rumfar akwati guda 6,652 a faɗin jihar.
Sai dai babban jam’iyyar adawa ta PDP ba ta shiga zaɓen ba saboda rikicin cikin gida da ta dabaibaye ta.
Jam’iyyun da suka shiga akwai APC, National Accord Party, AAC, ADC da Booth party.