Hukumar Zaɓe za ta yi wa ma’aikatan ta bita kan aikin faɗakarwa

Daga FATUHU MUSTAPHA

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za ta shirya wata bita ta musamman domin wayar da kan ma’aikatan ta na sashen faɗakar da masu zaɓe da ke hedikwatar ta da kuma jihohi.

Wata sanarwa da ta fito daga hukumar a ranar Asabar ta ce bitar, mai taken “Faɗakar da Mai Faɗakarwa”, wato “Train-the- Trainers (ToT)”, an kasa ta zuwa gida biyu saboda matsalar annobar korona (COVID-19) da ake fama da ita.

Kashin farko za a yi bitar ga shugabannin sashen faɗakar da masu zaɓe (HODs VEP) da ke jihohin Kudu da kuma waɗanda su ke a hedikwata a Abuja. Za a yi nasu daga ranar 1 zuwa ranar 3 ga Maris, 2021 a otal ɗin ‘Royal Bird Hotel’ da ke unguwar Alagbaka, GRA, Akure, Jihar Ondo.
 
Kashi na biyu na bitar za a yi wa shugabannin sashen faɗakar da masu zaɓe (HODs VEP) da ke jihohin Arewa da na hedikwata da ke Abuja daga ranar 11 zuwa ranar 13 ga Maris, 2021 a garin Lokoja, Jihar Kogi, amma ba a tsaida wurin da za a yi ta ba.

Haka kuma wannan bita, wadda za a shirya ta ne tare da haɗin gwiwar Gidauniyar Tsare-tsaren Zaɓe ta Duniya (International Foundation for Electoral Systems, IFES), za ta amince da Kundin Wayar da Kan Masu Zaɓe wanda jami’an Hukumar Zaɓe da ke hedikwata su ka riga su ka kammala duba shi.
 
Bugu da ƙari, bitar za ta bada dama a bayyana wa shugabannin sashen faɗakarwar ayyukan da hukumar ta sanya a gaba da su ka haɗa da: faɗaɗa hanyar da masu zaɓe za su samu isa ga rumfunan zaɓe; da aikin cigaba da yi wa masu zaɓe rajista wanda ke tafe; da Babban Shirin 2022-26; da batun zaɓen gwamnan Jihar Anambra; da kuma yin musayar ra’ayi kan abubuwan da su ka gudana a lokacin Babban Zaɓen da aka yi a shekarar 2019.