Hukumar Zakka ta Katsina ta karɓi rahoton rabon amfanin gona na gundumar Ƙaramar Ƙafur

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Hukumar Zakka da Waƙafi ta Jihar Katsina ta karɓi rahoton rabon zakkar kayan noma buhu 6200 da adadin su ya kai kimanin Miliyan 372 daga Ƙafur a ƙaramar hukumar Ƙafur .

Babban sakataren hukumar Dakta Abubakar Yusuf ne ya karɓi rahoton a madadin shugaban hukumar daga hakimin Ƙafur kuma Ɗan Galadiman Katsina Alhaji Abdul Rahman Rabe a garin Ƙafur.

Hakimin a jawabin sa wajen bikin miƙa rahoton ya bayyana cewa masarautar sa tayi tsarin faɗakar da manoma mahimmancin Zakka.

Ya bayyana cewa suma magadai da Limamai sun taka rawar gani wajan faɗakar da manoma a yankin da hakan ya sanya manoma suka rinƙa ba da zakkar ,wasu ma a gonakin su aka raba ta ganin cewa ba a jinkirin ta.

Hakimin yayi fatan wannan shekara hukumar da kanta za ta yi wannan rabon domin su shaida ƙasar Ƙafur ƙasar noma ce .

Ɗan Galadiman ya ƙara da cewa akwai waƙafi da suka bayar na gona domin ayi lambu”wanda da kanmu muke zuwa muyi aikin dashen lambu domin samun yardar Allah”ya ce.

Ya bayyana cewa shi wannan lambu sun bada shi ne ga marayu da masu buƙata na musamman.

Hakimin yayi wa hukumar Zakka ta jihar da Waƙafi na makarantar islamiyya da wani bawan Allah ya gina wa marayu da kuma waƙafi na maƙabarta ya bayar duka a garin Ƙafur.

A jawabin sa bayan da ya amshi rahoton, babban sakataren hukumar Dakta Abubakar Yusuf yayi bayani mai tsawo kan mahimmancin zakka da waƙafi tare da yabawa manoma da suka bayar da wannan zakka.

Sai yayi kira da sauran manoma da suyi koyi da ƴan uwansu manoman na garin ƙafur wanda yace Allah ne ya umurci ayi haka.