Daga AMINA YUSUF ALI
‘Yan kwamitin shugaban ƙasa a kan haraji da gyara al’amurran tattalin arziki na Nijeriya sun bayyana cewa, daga yanzu hukumar Kwastam da sauran hukumomi da ma’aikatu guda 62 na gwamnatin Tarayya za su daina amsar haraji kai-tsaye.
Shugaban kwamitin mai suna, Taiwo Oyedele, shi ya yi wannan jawabi a wata tattaunawarsa da gidan talabijin ɗin Channels Television a wani shiri da suka saba gudanarwa duk ranar Laraba. Ya ƙara da cewa, hukumar tattara haraji ta tarayya ita ce za ta cigaba da harajin dukkan waɗannan hukumomi da ma’aikatu.
Oyedele, ya bayyana cewa, Nijeriya tana daga cikin ƙasashe ma fi ƙarancin haraji kuma amma kuɗin da ake kashewa wajen karɓar yana da yawa.
A cewar sa, Nijeriya tana da ma’aikatu da hukumomi guda 63. Kuma a cewar sa waɗannan hukumomi suna samun rabuwar hankalinsu wajen yin ayyukansu sannan kuma su amshi haraji.
Sannan kuma abu na biyu a cewar sa, waɗancan ma’aikatu ba a yi su don su dinga amsar haraji ba, shi ya sa ba sa iya amsar harajin yadda ya kamata.
“Don haka, mayar da alhakin tattara harajin ga hukumar FIRS yana da alfani har guda biyu. Za a samu ingancin kuxin da ake kashewa wajen tattara harajin sannan jajircewar tattarawar za ta ƙaru, sannan kuma waɗannan ma’aikatu za su mai da hankali a kan ayyukansu, shi kuma tattalin arziki zai rabauta a sakamakon haka”.
Don haka ya yi kira ga dukkan hukumomin da ma’aikatun da su mayar da hankali a kan aikinsa domin ba a tsara su don su tattara haraji ba FIRS za ta amshi wannan aikin.
Kuma a cewar sa, hakan zai tabbatar da an tattara harajin cikin gaskiya da riƙon amana.