Hukuncin Kotu: Za mu ƙwato ‘yancinmu a Kotun Ɗaukaka Ƙara – Gwamna Yusuf

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ce za su ɗukaka ƙara domin ƙwato ‘yancensu.

Kszalika, yi kira ga al’ummar jihar da a zauna lafiya, tare da shan alwashin zai yi amfani da hanyar shari’a wajen maido da nasarar da aka ƙwace masa.

Manhaja ta rawaito a Larabar da ta gabata Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Gwamnan Kano ta yanke hukunci kan shari’ar da ke gabanta inda ta ce Yusuf Gawuna ne zaɓaɓɓen Gwamnan Kano amma ba Yusuf Kabir ba.

Kotun ta bada umarnin a janye shaidar lashe zaɓen da aka bai wa Abba Kabir na Jam’iyyar NNPP sannan a miƙa wa Gawuna na APC.

Sa’ilin da yake yi wa manema labarai bayani, Gwamna Yusuf ya ce hukuncin da kotun ta yanke cike yake da kurakurai, wanda a cewarsa yana da tabbacin za a iya gyara kurakuran a kotun ɗaukaka ƙara.

“Al’ummata ta Jihar Kano, idan ba ku manta ba kun yi fitar farin ɗango a ranar 18 ga Maris, 2023 kuka zaɓe ni a matsayin gwamnanku da ƙuri’u 1,019,602 da ratar ƙuri’u 128,897 tsakanina da wanda ya zo na biyu.

“Sannan aka rantsar da ni a matsayin zaɓaɓɓen Gwamna ran 29 ga Mayu, 2023. Haka nan, idan ba ku manta ba jam’iyyar da ta sha ƙasa a zaɓen ta kai mu kotu.

“Sai dai, bayan shafe watanni shida ana sauraren shari’ar a Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen gwamnan jihar, yau Laraba, 20 ga Satumba, 2023, alƙalan kotun sun yanke hukunci cikin hikimarsu.

“A matsayin ‘yan Adam, ba lalle ne ba hukuncin nasu ya zama daidai ɗari bisa ɗari, akwai kurakurai da rashin ajiye doka a mazauninta kamar yadda lauyoyinmu suka faɗa.

“Wannan ya sa kundin tsarin mulkin ƙasarmu ya samar da sauaran matakan da za a bi idan irin haka ta faru, kamar shiga Kotun Ɗaukaka Ƙara da Kotun Ƙoli,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, “Mun riga mun sanar da lauyoyinmu su ɗaukaka ƙara ba da ɓata lokaci ba don tabbatar da an yi adalci.”

Daga nan, Gwamna Yusuf ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da a zauna cikin lumana da kiyaye dokoki kasancewar an tura jami’an tsaro don ba da cikakkiyar kariya ga rayuwa da dukiyoyin al’ummar jihar.