Hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara: Za mu haɗu a Kotun ƙoli – Abba

Daga BASHIR ISAH

A matsayin ɓangare na fafutukar da yake yi na ganin ya kare kujerarsa a matsayin Gwamnan Kano, Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ce zai garzaya Kotun Ƙoli domin kuwa bai gamsu da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yanke na korar shi daga kan kujerarsa ba.

A ranar Juma’a ce Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bi sawun Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓe wajen soke nasarar da Abba Kabir na jam’iyyar NNPP ya samu zaɓen gwamnan Kano da ya gudana a watan Maris da ya gabata, sannan ta ayyana ɗan takarar APC, Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin halastaccen zaɓaɓɓen Gwamnan Jihar.

Da yake mayar da martani a wani faifan bidiyo da maraicen Juma’a, Gwamna Abba ya ce ba a yi musu adalci ba a hukuncin, amma za su ɗaukaka kara.

A cewarsa, “Wannan kotun, kamar ta baya ma ba ta yi mana adalci ba. Mutanen Kano sun zaɓe mu, amma waɗannan kotunan sun ce waɗancan mutanen ne suka ci.”

Ya ci gaba da cewa, “Tuni mun umarci lauyoyinmu da su shigar da wata sabuwar ƙara a Kotun Ƙoli ta Nijeriya. Muna kyautata zaton wannan kotun za ta yi wa al’ummar Jihar Kano adalci ta hanyar dawo musu da abin da suka ƙwata,” in ji Abba.

Gwamnan ya kuma bai wa mutanen Jihar tabbacin cewa za su haɗa kai da jami’an tsaro domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyinsu.