Ibadan: EFCC ta gurfanar da dattijo gaban kotu kan zambar kuɗin fili milyan N25

Daga WAKILINMU

Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC) ta shiyyar Ibadan, ta gurfanar da wani dattijo ɗan shekara 68 a gaban kotu bisa zargin zambar kuɗaɗen fili har naira milyan 25.

EFCC ta gurfanar da Ezekiel Oluwadare James a gaban Mai Shari’a Patricia Ajoku ne kan laifuka guda biyu, wato haɗin baki da kuma samun kuɗi ba ta hanyar da ta dace ba. Wanda a cewar hukumar hakan ya saɓa wa sashe na 8(a) na dokokin zamba da sauran laifuka masu alaka da haka na 2006, wanda hakan ya cancanci horo a ƙarƙashin kashi na 1 (3) na dokar.

Hukumar ta ce dattijon ya kitsa damfara inda ya saida wa wani fili sannan ya karɓi kuɗi naira miliyan 25 a hannunsa.

Yayin da kotu ta karanto masa laifukan da ake tuhumarsa da aikatawa, Oluwadare ya ƙi amsa aikata laifukan.

Daga nan Mai Shari’a Ajoku ta ɗage shari’ar zuwa 24 ga Maris, 2021 inda za ta saurari batun belin da wanda ake zargi ya nema, sannan ta yanke hukunci a ran 26 ga Afrilu, 2021.

Alƙaliyar kotun ta bada umarnin a tafi da dattijon a tsare shi a gidan gyaran hali da ke Abolongo a garin Oyo har zuwa lokacin da za a bada belinsa.