ICPC ta ɓullo da dabarun duba ayyukan mazaɓu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta ta ICPC, ta ce ta ɓullo da dabaru domin hana ’yan siyasa da sauran masu ruwa da tsaki babakere a harkokin mazaɓu.

An ruwaito cewa Shugaban Hukumar, Dakta Musa Adamu Aliyu (SAN) ya bayyana haka ne a ranar Larabar da ta gabata a wata ganawa da editocin kafafen yaɗa labarai na arewacin Nijeriya, inda ya bayyana matakan da suka dace da hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ɗauka na hana tafka maguɗi a ayyukan mazaɓu da dai sauransu.

A cewar shugaban, a duk lokacin da aka gabatar da kasafin kuɗin ga majalisar ƙasa, “muna ƙoƙarin yin nazari a kan kasafin kuɗin, ta yadda za mu sani idan akwai wasu kuɗaɗen da aka bi wasu hanyoyin da su.

“Har ila yau, a kodayaushe muna ƙoƙarin ganin idan akwai wasu abubuwan da aka sanya a cikin kasafin kuma muna yin nazari akai-akai domin mu tabbatar da cewa babu wata maƙarƙashiya acikin kasafin kuɗin,” inji Aliyu.

”Saboda haka idan muka lura da irin wannan matsalar, muna ziyartar ofishin kasafin kuɗi don samun ƙarin haske”.

Daga baya mu kan hana irin sakin waɗannan kuɗaɗe a duk lokacin da abin ya faru.’’

A halin da ake ciki, Dokta Musa Aliyu ya ce bisa hukuncin da kotun koli ta yanke na bai wa ƙananan hukumomi ’yancin cin gashin kansu, hukumar na haɗa gwiwa da ƙungiyoyin fararen hula masu sahihanci don aiwatar da shirin rigakafin cin hanci da rashawa ga ƙananan hukumomi don tabbatar da fara bayyana shirye-shiryen da suka shafi kuɗi, saye da kuma daƙile cin hanci da rashawa.”

Shugaban ICPC ya ce abubuwa uku ne ke taimakawa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa.

Ya ce dole ne mutum ya zama mai ilimi, ya kasance mai rion amana da jajircewa wajen sauya al’umma zuwa ga alheri.

Tsohon babban lauyan gwamnatin jihar Jigawa kuma babban lauyan Nijeriya, (SAN) ya bayyana cewa manufar ICPC ta gindaya, ‘CARE’ wanda ke nufin Al’adu, da bin ƙa’ida, dawainiya da nagarta na taimakawa wajen gudanar da ayyukan hukumar cikin kwazo.

Ya kuma yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su hada kai da hukumar domin wayar da kan al’umma da inganta shirye-shiryen ICPC domin ci gaban ƙasa ya dogara da ita.