ICPC ta koka kan yadda ake karkatar da kuɗaɗen jama’a

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa Mai Zaman Kanta, ICPC, ta yi tsokaci jiya Alhamis a Abuja kan yadda ake karkatar da kuɗaɗen jama’a.

Shugaban hukumar ta ICPC, Farfesa Bolaji Owasannoye ne ya yi wannan tsokaci a wajen wani taron ƙara wa juna sani na kwana biyu da mambobin kwamitin majalisar wakilai kan yaƙi da cin hanci da rashawa suka gudanar.

Shugaban ya fusata kan yadda ake karkatar da kuɗaɗen jama’a, ta hanyar karɓar kuɗaɗen shiga da kuma kashe kuɗaɗe, yayin da ya yi Allah-wadai da yadda ake tafiyar da harkokin kuɗi ba bisa ƙa’ida ba, da karkatar da kuɗaɗe da kuma kasafin kuɗi.

Ya ce lokaci ya yi da za a fuskanci cin hanci da rashawa, ya ƙara da cewa har yanzu ‘yan Nijeriya ba su gane illar da cin hanci da rashawa ke da shi ba.

Ya yi gargaɗin cewa idan ‘yan ƙasar ba su tunkari matsalar cin hanci da rashawa ba, hakan zai ƙara yin illa ga ƙasar.

Mista Owasannoye ya bayyana cewa Nijeriya ba ta tava fuskantar qarancin dokokin yaƙi da cin hanci da rashawa ba, sai dai ta gaza wajen tabbatar da gaskiya. Ya kuma yi nuni da cewa, munafurci ya ƙara ta’azzara hakan.

A cewarsa, CBN, ofishin kula da harkokin gwamnati da kuma hukumar kula da gasa da masu amfani da kayayyaki ta tarayya, duk jami’an tsaro ne na yaƙi da cin hanci da rashawa.

Ya bayyana cewa galibin hukumomin da suka dace suma sun taka rawa wajen yaƙi da cin hanci da rashawa.

Mista Owasannoye ya lura cewa cin hanci da rashawa na ƙara nuna goyon bayan siyasa tare da ƙarfafa yin zagon ƙasa ga gwamnati, yana mai jaddada cewa ba a tava amfani da kuɗazen da aka ware a takarda ba don manufar da ake nufi da su.

A nasa jawabin shugaban kwamitin yaƙi da cin hanci da rashawa na majalisar, Shehu Garba ya bayyana cewa ƙalubalen da yaqi da cin hanci da rashawa ya kasance wani batu na kan gaba.

Ya ce an yi rubuce-rubuce da yawa kan illolin cin hanci da rashawa, ya ƙara da cewa ‘yan Nijeriya ba sa buƙatar a tuna musu da illar da hakan zai haifar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *