Daga AHMAD FAGAM
Ko shakka babu, duniyar bil adama tana fama da tarin ƙalubaloli waɗanda ke zama barazana ga zaman lafiya, da tsaro, da walwala, har ma da ci gaban duniyarmu baki ɗaya.
Musamman idan muka yi la’akari da yadda duniyarmu ke fuskantar tarin matsaloli, kamar matsalar karayar tattalin arzkin sassa daban-daban na duniya, da matsalar sauyin yanayi wanda ke kara jefa rayuwar dan adam da sauran halittu gami da shi kansa muhallin halittun cikin garari, ga kuma matsalar annobar COVID-19 da ake fama da ita, sannan uwa uba ga matsalar yawaitar tashe-tashen hankula a sassa daban-daban na duniya.
Sai dai abin takaici ne, yayin da wata ƙasa ke yin bakin ƙoƙarinta wajen bada gagarumar gudunmawa domin ceto rayuwar bil adama daga cikin mawuyacin hali, amma wasu ƙasashen suna rufe idanunsu suna mantawa da dukkan alkhairan da wata kasa ke yi wajen kyautata rayuwar bil adama.
Alal misali, yayin da ƙasar Sin ke cigaba da ƙoƙarin neman kyautata rayuwar al’ummarta har ma da sauran al’ummun duniya baki ɗaya, don samar da kyakkyawar makomar bil adama, amma wasu ƙasashen yamma na kokarin siyasantar da dukkan ƙoƙarin da ƙasar Sin ke yi na kyautata rayuwar dan adama.
A baya bayan nan, ƙwararru masanan kasar Sin sun soki lamirin ’yan siyasar ƙasar Amurka masu adawa da ci gaban ƙasar Sin, waɗanda ke shirya maƙarƙashiya da makirci domin hana al’ummar yankin Xinjiang damamamkinsu na cigaba ta hanyar yada ƙarairayin cewa, wai ana tilasta aikin ƙwadago a shiyyar. Masanan dai sun yi Allah wadai da wannan aniyar Amurkawan masu fakewa da siyasa.
Cao Wei, wani malamin jami’ar Lanzhou, ya bayyana cewa, wasu kamfanoni na fargabar kakkaba takunkumi daga ƙasar Amurka, hakan ya sa wasu daga cikin kamfanoni ba su son ɗaukar ma’aikatan ƙwadago ’yan ƙabilar Uygur, inda hakan ke haifar da ƙaruwar rashin ayyuka yi da kuma haifar da koma bayan ci gaban yanayin zaman rayuwar al’ummar Uygur.
Shi ma Ildos Murat, mataimakin shugaban tarayyar ƙungiyoyin ’yan kasuwan yankin Xinjiang, ya bayyana cewa, gaskiyar magana shi ne, Amurka ita ce ƙasar da har yanzu ayyukan ƙwadago na tilas ke cigaba da wanzuwa har a wannan karni na 21, yayin da ’yan ci rani su ne matsalar ta fi shafa, kuma gwamnatin Amurka ta kawar da kanta daga sauke haƙiƙanin nauyin dake wuyanta wajen ba su kariya.
Ko shakka babu, za mu iya cewa, ƙoƙarin da kasar Sin ke yi wajen kyautata rayuwar al’ummun yankin Xinjiang, da sauran sassan ƙasar, har ma da sauran ƙasashen duniya, musamman ƙasashe masu tasowa, abin a yaba mata ne, kuma “idan amarya ba ta hau doki ba, bai kamata a dora mata kaya ba.”