Idan ba za a taimaka wa Afghanistan ba, bai kamata a yi mata fin ƙarfi ba

Daga CRI HAUSA

Idan aka kira Afghanistan, na yi imanin babu abun da zai zo zuciyar mutane fiye da yaƙe-yaƙen da ta yi fama da su da ɗimbin wahalhalun da jama’arta ke fuskanta. Sai dai, abun mamaki, a wannan gaba da ƙasar ke cikin mawuyacin hali ne, gwamnatin Amurka ta sanar da cewa za ta saki wasu kuɗaɗen ƙasar da a baya ta ƙaƙabawa takunkumi, waɗanda yawansu ya kai dala biliyan 7, inda za ta yi amfani da rabinsu wajen biyan diyya ga mutanen da harin ranar 11 ga watan Satumban 2001 ya rutsa da su.

Idan ba a manta, al’ummar Afghanistan sun shafe gomman shekaru suna fama da yaƙi, haka zalika, Amurka ta kwashe shekaru 20 da sunan tana yaƙi da ’yan ta’adda a ƙasar. Kuma janyewar da ta yi a baya-bayan nan cikin watan Augustan bara, ya sa ƙasashen waje ƙaƙaba takunkumi kan kuɗaɗen ajiyar ƙasar da yawansu ya kai dala biliyan 10, kuma dala biliyan 7 daga ciki, yana Amurka. Wannan yunquri kaɗai ya durƙusar da tattalin arzikin ƙasar Afghanistan tare da jefa al’ummarta cikin mawuyacin hali.

Ƙasashe da hukumomin duniya na ta kira da a kare tattalin arzikin ƙasar daga durƙushewa. Ko yayin taron ƙungiyar haɗin kan Shanghai SCO da aka yi a watan Satumban da ya gabata, shugaban ƙasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shawarwarin taimakawa ƙasar. Shi ma Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres ya yi irin wannan kira a watan Oktoba. Haka zalika ƙungiyar IOC ta ƙasashen musulmi, cikin watan Disamba, ta kafa asusun tallafawa al’ummar Afghanistan.

Abun takaici ne yadda Amurka ke kiran kanta da babbar ƙasa kuma mai martaba tsarin demokraɗiyya, ke ɓullo da hallayar da suka saawa furucinta, waɗanda ke bayyana irin son kai da rashin imaninta da kuma danniya ko fin ƙarfi. Arzikin ƙasar Afghanistan, mallakin al’ummar ƙasar ne, su ne ya kamata a ce sun kasafta arzikinsu yadda ya dace a matsayin ƙasar na mai cikakken ’yanci, ba wai wata ƙasa ta nuna musu fin ƙarfi ba.

Ayyukan ta’addanci ta kowacce fuska, ba abu ne da za a lamunta ba. Babu wanda zai goyi bayan munanan hare-haren da aka kai wa Amurka a ranar 11 ga watan Satumba, haka kuma ba za a manta da waɗanda hare-haren suka rutsa da su ba. Amma, bai kamata ɗaukacin al’ummar Afghanistan su ɗauki alhakin abun da wasu ’yan tsiraru suka yi ba.

Idan har Amurka ba za ta taimaka wa ƙasar fita daga mawuyacin halin da take ciki, wadda ta taimaka wajen ingiza ta ba, to bai kamata ta ce za ta ɗauki rabin dukiyarta ko kuma ta zama mai sarrafa dukiyar ƙasar ba. Sam wannan bai dace ba, domin fin ƙarfi ne.