Idan da goyon baya mata kaɗai na iya ciyar da ƙasa – SWOFON

Daga BASHIR ISAH

Kodinetar Ƙungiyar Ƙananan Manoma Mata (SWOFON) ta jihar Bauchi, Hajiya Marka Abbas, ta ƙarfafa cewa mata kaɗai na iya ciyar da ƙasa muddin suka samu goyon bayan da suke buƙata.

Marka ta bayyana haka ne a wajen wani taron musayar ra’ayi game da harkokin noma, shiryawar ƙungiyar ‘Fahimta Women and Youth Development Initiative’ (FAWOYDI) tare da haɗin gwiwar ActionAid Nigeria, wanda ya gudana ran Litinin, a Bauchi.

A cewarta mata sun fi maza iya tattali ta yadda za su iya amfani da kayan aiki kaɗan wajen samar da amfani mai yawa.

Don haka ta yi kira ga gwamnati kan cewa ta riƙa tunawa da mata manoma a duk lokacin da take shirya kasafin fannin harkokin noma, da kuma lissafawa da su wajen rabon kayan aikin gona kamar takin zamani da sauransu.

Da yake tofa albarkacin bakinsa yayin taron, Manajan Ayyuka na Shirin Bunƙasa Harkokin Noma na Jihar Bauchi, Alhaji Jafaru Ilelah, ya yaba wa waɗanda suka shirya taron, yana mai cewa sun yi abin da ya kamata kuma a kan lokacin da ya dace.

Ya ce hukumarsu za ta yi aiki tare da hukumomi masu zaman kansu wajen bunƙasa fannin moman jihar kasancewar gwamnati ita kaɗai ba ta iyawa.