Idan ka cika namiji ka fito lokacin harin ‘yan ta’adda a garinku, inji Masari

Daga UMAR GARBA a Katsina

Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari ya ƙalubalanci al’ummar jihar akan su daina ɓoyewa cikin gidajensu idan ‘yan bindiga sun kawo hari a garuruwansu, madadin hakan ya buƙaci al’umar jihar da su fito su tunkari ‘yan bindigar a duk lokacin da suke aikin ta’addanci a jihar.

Masari ya bayyana hakan ne a gidan gwamnatin Muhammadu Buhari da ke zama fadar gwamnatin jihar Katsina a lokacin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai.

“Idan kai namiji ne ka fito da dare mana lokacin da ‘yan ta’adda suka kawo hari ba wai ka ɓoye ba da rana kuma ka tare hanya ka hana matafiya wucewa, wannan ba daidai ba ne,” inji shi.

Sai dai ana alaƙanta waɗannan bayanai na Gwamna Masari akan wasu matasa dake fitowa su kuma tare hanyoyi da sunan zanga-zanga bayan ‘yan bindiga sun kai hare-hare a ƙananan hukumominsu.

Masari ya kuma jaddada kiran da ya yi wa al’ummar jihar akan su tashi tsaye don kare kawunan su daga ‘yan bindiga dake addabar wasu daga cikin ƙananan hukumomin jihar, inda ya buƙaci al’ummar jihar da su mallaki makamin kare kawunansu.

Ya ƙara da cewa gwamnatin sa a shirye take don taimaka wa al’ummar jihar akan yadda za su mallaki makami na kare kan su, ya kuma ce  ‘yan sanda a shirye suke don yi wa waɗanda ke son mallakar makami rajista a jihar.

Masari ya bayyana cewa kiran ya zama wajibi duba da yawan ‘yan sanda da ake da su a  jihar ba za su iya samar da tsaro ba saboda yawan su bai wuce dubu uku ba a cikin jimillar yawan mutane miliyan takwas dake zaune a faɗin jihar. 

“Yan sanda nawa muke da su? Sojoji nawa mu ke da su? Yawan ‘yan sanda a Katsina ba ya wuce dubu uku cikin mutum miliyan takwas da ke zaune a jihar,” inji shi.

Masari ya kuma bayyana cewar duk wanda ‘yan bindiga su ka hallaka a ƙoƙarin kare kansa ya yi shahada.

“Idan an kawo mana hari mu ka fita don kare kai idan an kashe mu ana kyautata zaton mun yi shahada.

“Allah bai ce ka kwanta ba akashe ka ko a wulaƙanta iyalan ka ko kuma a ƙwace maka dukiya idan ka rasa ranka a ƙoƙarin kare kan ka jihadi ka yi,” inji Masari.

Ya kuma ce bai kamata mutanen banza (‘yan bindiga) su riƙe makami ba amma mutanen kirki (al’ummar jihar) su ƙi neman makamin da za su kare kan su ba, don haka ne gwaman ya buƙaci al’ummar jihar da su nemi makami don kare kawunan su.

Daga ƙarshe gwamnan ya bayyana cewar ‘yan bindiga ba sa la’akari da bambancin addini ko jam’iyyar siyasa ko kuma ƙabila, sukan kashe duk wanda su ka samu su kuma ƙwace masa dukiya, saboda haka ne ya roƙi al’ummar jihar akan su taimaka wa gwamnati wajen samar da tsaro a jihar da ma ƙasar bakiɗaya.