Idan ka ga marubuci yana rubutu ba ya samun kuɗi shi ya so – Sadik Lafazi

“Wasu ƙungiyoyin ba sa son ɗaukar sabon marubuci”

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

Baƙon marubucin mu na wannan mako shi ne Malam Sadik Abubakar Abdullahi, shugaban ƙungiyar Lafazi Writers Association, ɗaya daga cikin fitattun ƙungiyoyin marubuta na onlayin da suke taka rawar gani wajen fitar da littattafai masu ƙunshe da basira da darussa masu yawa, da kuma kiyaye ƙa’idojin rubutun Hausa. Ya kasance daga cikin maza marubuta da suka zama tamkar madubi ko ababen koyi ga matasan marubuta masu tasowa. A zantawarsa da wakilin Blueprint Manhaja Abba Abubakar Yakubu ya bayyana masa yadda yadda shi da wasu marubuta suka kafa ƙungiyar Lafazi Writers Association, don magance wasu matsaloli da suke faruwa da wasu ƙungiyoyin marubuta a baya. A sha karatu lafiya.

MANHAJA: Ka gabatar mana da kanka.

SADIK: Sunana Sadik Abubakar Abdullahi, ni marubuci ne kuma manazarcin littattafan Hausa. Malamin makarantar boko, sannan kuma mai sana’ar buga takardu da aikin sarrafa na’urar zamani, wato Computer Business Centre.

Ko za ka gaya mana tarihin rayuwarka?

An haife ni a garin Gwagwarwa da ke cikin ƙaramar Hukumar Nassarawa, a Jihar Kano. Na fara karatun addini daga baya na shiga makarantar boko, har zuwa matakin digiri. Na fara ne da karatun a makarantar firamare ta Gwagwarwa Special, daga nan na shiga ƙaramar Sakandire a cikin Makarantar Sakandiren Gwamnati da ke nan Gwagwarwa. Na wuce Kwalejin Gwamnati ta Kano, wato tsohuwar KTC.

Bayan na rubuta WAEC na wuce mataki na gaba, inda na nemi gurbin karatu a makarantu biyu, Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Kano da kuma Kwalejin Ilimi ta Tarayya wato FCE Kano. Sai kuma Allah Ya nufa na samu FCE ɗin, inda na karanta fannin koyar da turanci da koyar da ilimin zamantakewa, English and Social Studies. Na fara aiki kafin daga baya na ɗora da karatun digiri koyar da ilinin harsuna ɓangaren harshen Turanci (B.ed Language Arts English, a nan FCE Kano.

Yaya tasowarka ta kasance, da irin gwagwarmayar da ka sha kawo yanzu?

Na taso cikin kulawar iyayena, baya ga makaranta da nake zuwa, a hannu guda kuma mahaifiyata na yin sana’ar da muke tallatawa gida-gida. Bayan na tasa kuma ta kai ni wajen koyon sana’ar gyaran babura, na koyi gyaran babura sosai kuma na jima a cikin sana’ar kafin daga bisani na bar ta a lokacin da na fara zuwa makarantar gaba da sakandire. A lokacin da kammala sakandire na shiga makarantar koyon sarrafa na’ura mai ƙwaƙwalwa.

Bayan na kammala sai na fara aikin wucin-gadi da wani shagon amfani da yanar gizo, wato cafe. Lokacin da na kammala NCE na fara koyarwa, a hannu guda kuma ina koyar da na’ura mai ƙwaƙwalwa, a ƙarƙashin wata qungiya mai suna Hausa Fulani Youth Development and Orientation Forum (HAFYDOF). Na horar da mutane da yawa ilmin na’ura mai ƙwaƙwalwa a ƙarƙashin wannan ƙungiya, ciki har da waɗanda ‘yan siyasa kan ɗauki nauyinsu. A yanzu haka ina koyarwa kuma ina cigaba da harkar Computer Business Centre.

Me ya ja hankalinka ka fara sha’awar rubuce-rubucen Hausa na adabi?

Abin da ya ja hankalina na shiga rubutu shi ne, yawan karance-karance littattafan Hausa, da yadda marubuta kan yi amfani da ƙwaƙwalansu wajen sauya tunanin al’umma cikin ruwan sanyi, da kuma yadda rubutu ya kasance sassauƙar hanyar yin jihadi da alqalami ba da takobi ba.

Wacce shekara ka fara rubutun adabi na kanka, kuma wa ya fara nuna maka yadda ake rubutun labari?

Gaskiya ba zan iya haƙiƙancewa ba, amma dai lokacin da ludayin Abdulaziz Sani Madakin Gini (Yaron Malam), ke kan dawo na fara rubuta labari irin nasa na yaƙe-yaƙe. Domin a wancan lokacin babu labarinsa da zai fito face na saya na karanta. Wasu lokutan ma iya kuɗin littafin ne kawai da ni, sai na tafi da ƙafa zuwa ‘Yan-Kura na sayo littafi na dawo gida na karanta.

To, bayan rasuwar Madakin Gini, ni ma sai na mutu a duniyar karatun littafi. Gabaɗaya sai na watsar, ko kaɗan ba na sha’awar karatun. Bayan wasu shekaru kuma sai na tsinci wasu littafin Sa’adatu Saminu Kankiya, mai suna ‘Son Zuciya’, da kuma littafin ‘Matar So’ na marigayiya Hadiza Salisu Sharif. Na saya na karanta, kuma a dalilin haka na sake dawowa ruwa, sai dai a wannan karon ba littattafan yaqi nake karantawa ba. Na fi karanta littattafan zamantakewa da matsalolin rayuwa sai na soyayya, wanda ba kasafai nake karanta su ba.

Za ka iya tuna labarin da ka rubuta na farko, kuma a kan me ka rubuta?

Labarin da na fara rubutawa na yaƙi ne kamar yadda na bayyana a baya, sai dai ban kammala shi ba. Da yake a lokacin ba wani muhimmanci na ba wa abin ba, don haka ma yanzu ba zan iya tuna shi ba sosai.

A lokacin da na sauya alqibilar karance-karancena, sai na fara rubuta wani labari shigen irin wanda nake karantawa. Littafin da na fara rubutawa a wannan fannin shi ne na sa wa suna, ‘Sahura’.

Shi labarin ‘Sahura’, na rubuta shi ne a kan jigon haquri. Labari ne na wata yarinya da take rasa iyayenta duka biyun a sanadiyar harin ‘yan ta’addan, sai wan mahaifiyarta ya ɗauko ta wajensa. Yana da mata, sai dai jininta bai haɗu da na ‘Sahura’ ba. Hakan ta sa ta riqa azabtar da ita, ba ta da sukuni ko kaɗan. Wan mahaifiyar bai sani ba kasancewar ba mazauni ba ne, haka ‘Sahura’ ta riƙa girbar uƙuba iri-iri tana haƙuri har ta riski kyakkyawan sakamakonta.

Kawo yanzu ka rubuta littattafai nawa, gajerun labarai nawa?

Na rubuta littattafai guda shida, a ciki akwai gajerun labarai masu yawa da ban san adadinsu ba.

Kawo sunayen littattafan da ka rubuta da taƙaitaccen bayani game da fitattu uku daga ciki. ‘Sahura’, ‘Matakin Nasara’, ‘Cikas’, ‘Ƙuda Ba Ka Haram’, ‘Kowacce Ƙwarya’, ‘Rayuwar Talaka’.

Littafin ‘Matakin Nasara’ yana ɗauke ne da labarin wasu tagwayen ‘yammata da suka taso a hannun iyaye masu ƙaramin ƙarfi, rayuwa ta riƙa tsananta gare su wanda a matsayinsu na mata masu ƙananan shekaru da su iyayen nasu suka haɗa kai don ganin sun gudu tare sun tsira tare. Ana cikin wannan yanayi ne kuma Ubangiji Ya jarabci mahaifinsu da cutar tsinkewar laka (spinal cord).

Rayuwa ta qara tsananta ainun a gare su, daga nan suka fara zuwa aikin kamfani ana biyan su lada, duka a lokacin ba su wuce shekara goma sha biyar ba. A wannan aikin ne kuma suka haɗu wani manajan kamfani mai halin ɗan’akuya. Ya nemi yin lalata da su, amma baƙar manufarsa ba ta tabbata ba. Bayan sun haƙura da aikin sun rungumi halin Annabawa, sai Ubangiji Ya sauya rayuwarsu kamar yadda Hausawa ke cewa ‘bayan duhu sai haske.’

Shi kuma littafin ”Ƙuda Ba Ka Haram”, labarin wani ma’aikacin ɗamara ne wanda ake musu laƙabi da abokin kowa, da salihar matarsa. Shi dai wannan ma’aikaci ya kasance mai hali irin na ƙuda, ga tsananin kwaɗayi. Ba ya tsoron haram ko kaɗan, bai san amana ba bare har ya riƙe ta. Neman mata kamar bunsuru, hakan ta sa har ƙanwar matarsa da suke yi uwa ɗaya bai ƙyale ba, sai da ya lalata mata rayuwa. Caca tamkar kartagi, cin-hanci a wurinsa halak ne.

Labarin ”Kowacce Ƙwarya”… Labarin wasu masoya ne, Zaliha da Abubakar. Suna matuƙar ƙaunar junansu, kasancewar ita tauraruwar ɗaliba ce ga shi tauraron. Abubakar ya kasance yana son Zaliha tun ba ta san kanta ba, yana koyar da ita a makarantar addini da ta zamani. Bayan ta girma ta kai munzali, kwatsam sai wani Alhaji mai taƙama da dattin aljihu ya yi kutse cikin rayuwarsu. Kuma ya samu amincewar mahaifiyar Zaliha, kasancewar ta irin makwaɗaitan iyayen nan. Duk kuwa da cewa ba rayuwar ƙunci take yi ba, babu abin da take nema ta rasa, zuciyarta ce dai babu wadata.

Wannan Alhaji sai da ya raba wannan daɗaɗɗiyar soyayya ya auri Zaliha, sai dai auren kawai aka yi amma bai samu farincikin da yake nema ba. Matsaloli da fitintinun da suka riqa kunno kai tsakanin matansa da amaryar tasa ya tilas ya haƙura ya sawwake wa ita Zaliha ɗin, muradinta ya cika ta auri Saddiƙunta.

Ka tava samun damar buga wani daga cikin littattafanka, ko kai ma ɗan onlayin ne?

A’a, ban buga ba saboda a lokacin da na yi yunqurin bugawar, ana tsaka da samun matsalar rashin cinikin littafi, sannan kuma an ɗan karkata zuwa ga wallafar onlayin. Sannan kuma akwai matsala ta bangaren ‘yan kasuwa, idan mutum ya kai littafinsa za su karɓa da alƙawarin za a sayar masa. Amma idan ya tafi sai su buga nasu kwafin su riƙa sayarwa, bayan wani lokaci idan mai littafi ya zo karɓar ciniki sai a ce masa babu ciniki sosai. To wannan na daga cikin dalilan da suka daƙile ƙudurina na buga littafi.

Wanne salo ka fi amfani da shi wajen rubuta labaranka, kuma me ya sa?

Na fi amfani da sassauƙan salo wajen rubutu, saboda a yanzu mutane komai sauƙi suke nema. Kasancewar Hausar ma a wannan zamani yin ta kawai ake yi, amma wasu zantukan sam ba fahimtar ma’anarsu ake yi ba. Sannan kuma salon bayar da labarin ma na fi amfani da salon tauraro wajen fage, shi ma ya fi sauƙin fahimta ga masu karatu, haka nan marubuci ma zai fi samun sauƙi ta yadda ba zai riƙa samun tsinkewar zaren labarin ba.

Shin ka taɓa shiga wata gasar marubuta, kuma wacce nasara ka samu?

Na shiga gasanni sosai da ake sawa marubuta, na samu nasarori sosai Alhamdulillahi. Na zo mataki na ɗaya gasar ƙungiyar marubuta ta Nobel Writers Association, a shekarar 2022 da labarina mai suna ‘Al’ ummata.’ Har wa yau a cikin wannan shekara ta 2022 na samu nasara a mataki na huɗu a gasar ƙungiyar marubuta ta Jarumai Writers Association da labarina mai suna ‘Ƙasata’. Sannan akwai wasu gasanni na hidimar bukukuwa da ake sawa da kuma na ‘yan siyasa duk ina shiga kuma ina samun nasara walau a matakin farko ko na biyu ko na uku.

Wanne abu ne ya faru da rayuwarka a harkar rubutu, wanda ba za ka manta da shi ba?

A dalilin rubutu abubuwa sun faru da ni sosai, ɗaya daga ciki shi ne yadda mambobin ƙungiyata suka ɗauke ni a matsayin mai haska musu hanya, har abin da bai shafi rubutu ba sukan nemi shawarata.

Su wanene gwanayenka a cikin marubuta, waɗanda ka ke iya zama ka karanta rubutunsu?

Sabbin marubuta su ne gwanayena, tabbas duk wanda ya zo da kishin son yin rubutu mai ma’ana don bunƙasa harshen Hausa da Hausawa, shi ne gwanina kuma shi ne wanda nake zama na karanta labarinsa.

Bamu labarin yadda aka yi ka kafa qungiyar marubuta ta Lafazi?

Ƙungiyar Lafazi Writers Association, ta samo asali ne daga tsohuwar ƙungiyar Pen Writers Association, wacce marigayi Dr. Zain ya jagoranta. Wato lokacin da matsalolin suka yi wa ƙungiyar ƙawanya ta kowacce fuska, ɓangaren shugabanci babu kulawa, babu sa’ido dangane da me mambobi suke rubutawa. Yayin da ƙorafe-ƙorafe suka yi yawa, sai wasu ‘yan tsiraru daga mambobin wannan ƙungiya suka yanke shawarar yin wani abin kirki. Waɗannan mambobi sun haɗa da ni da Hassana Ɗanlarabawa da Fadila Lamiɗo tare da wasu sabbin mambobi muka magantu kan matsalolin da ke damun wannan ƙungiya.

Daga nan muka zauna muka tattauna mafita, daga ƙarshe muka cimma matsayar kafa ƙungiyar Lafazi Writers Association. Mu uku ne muka jagoranci ƙungiyar tun farko kamar yadda na faɗa wato ni da Hassana da kuma Fadila. Daga baya Billy Galadanci ta kafa wata ƙungiya ta mata zalla, sai suka yi ƙaura zuwa can. Ni kuma na ci gaba da jagorantar Lafazi Writers da tallafawar wasu daga cikin mambobi kamar Hajiya Surayya Dahiru da Hajiya Fauziyya Sani Jibril da sauran su.

Da mutane nawa aka fara, kuma kawo yanzu mambobi nawa ku ke da su?

Kamar yadda na faɗa a baya, mu uku muka fara kafa wannan ƙungiya ta Lafazi Writers Association, ni Sadik Abubakar Abdullahi, Hassana Ɗanlarabawa, da Fadila Lamiɗo. Kuma kamar yadda ka nemi ka sani a halin yanzu Lafazi na da jimillar mambobi talatin ne.

Menene ka ke ganin ya bambanta ƙungiyar Lafazi da sauran ƙungiyoyin marubuta na Hausa?

Yawancin ƙungiyoyin marubuta ba sa samun lokacin shirya bita ga sabbin mambobinsu, wasu qungiyoyin ma ba sa son ɗaukar sabon marubuci wanda bai san harkar adabi ba. To, ita kuma Lafazi Writers, yana daga cikin manufofinta ba da horo ga sabbin mambobi domin su riƙa rubutu bisa tsari da qa’ida. An sha turo mini sabbin marubuta da suka yi yunƙurin shiga wasu ƙungiyoyin, sai a ce indai suna son su koyi rubutu mai inganci to, su shiga Lafazi.

Waɗanne abubuwa ku ke yi a matakin ƙungiya wanda ke taimakawa mambobinku su samu ƙarin gogewa a harkar rubutu da shiga gasanni?

Muna ba da horo a ɓangarorin adabi da harshen Hausa da al’ada sosai. Muna bayar da darussan dabarun ƙirƙirar labari mai nagarta, muna da sashen koyar da ƙa’idojin rubutun daidaitacciyar Hausa, da kuma tarihi da al’adun Hausawa. Duka wannan don mambobi su san asalin al’ummar da suke yin rubutun domin su.

Shin akwai wasu nasarori da za ka iya cewa, ƙungiyar Lafazi ta samu ko mambobinta da ya kamata duniya ta sani?
Babu shakka akwai nasarori da dama, ƙungiya ta yi nasarar koyar da mutane da dama yadda ake rubutun labari mai ƙayatarwa. Ta shiga gasanni na kungiyoyi kuma ta samu kambun karramawa. Mambobinta sun samu nasarori sosai da suka haɗa cin gassanni marubuta daban-daban da ɗaukaka a duniyar marubuta. AlhamduliLlah.

Wanne tasiri ka ke ganin ƙungiyoyin marubuta ke da shi ga cigaban harkokin adabi a ƙasar nan?

Ƙungiyoyin marubuta na taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa harshen Hausa da al’adu. Suna taimakawa matuƙa wajen ganin alqaluman mambobinsu sun rubuta littattafai da za su taimaka wa al’umma da ƙasa bakiɗaya. Hukumomin Adabi da dama sun fahimci tasirin ƙungiyoyin marubutan nan, shi yasa ma kullum ake ƙara gano tasirin ƙungiyoyin wajen cigaba adabin.

Menene ya haɗa ka da kamfanin Bakandamiya Hikaya masu manhajar tallata littattafai?

A lokacin da aka samu cigaban wallafa littatafai a yanar gizo, ta yadda mutum zai iya yin amfani da wayarsa ya rubuta littafi cikakke, sai ni ma na yi sha’awar hakan. To, a lokacin na buɗe shafina a tsohon manhajar sada zumunta na Bakandamiya, a nan ne na haɗu da shugabar kula da harkokin manhajar, Hajiya Ramatu Lawan, wacce ita ce ta kai ni shafinsu na WhatsApp. Daga nan na ci gaba da aikace-aikacena ina kuma bibiyar na wasu.

To, daga bisani kuma sai mamallakin manhajar, Alhaji Lawan Ɗalha, ya tuntuve ni cewa za a buɗe wani sashe a Bakandamiya wanda zai dawo da sha’awar karatu a zukatan jama’a. Mu uku muka fara jagorantar wannan sashen mai suna Bakandamiya Reading Club, ina matsayin Sakatare daga baya kuma aka ƙaro mutum biyu domin duba da yawancin aikace-aikacen da muke yi.

Wanne tsari ku ke da shi a Bakandamiya da marubuta za su iya cin moriyarsu?

A halin yanzu an sauya sunan daga Bakandamiya Hikaya, ya koma Hikaya kawai. Hikaya ita ce manhajar farko ta raba marubutan Hausa, musamman na onlayin da yin rubutun kyauta tare da daƙile satar littafi. Tun daga samar da Hikaya kawo yanzu idan ka ga marubuci yana rubutu kyauta ba ya samun kuɗi, ko kuma ana satar masa littafi to shi ya so. Hikaya tana da tsarin da marubuci zai sayar da littafinsa ya samu kuɗaɗe sosai. Duk mai buƙata sai ya nemi manhajar mu ya sauke ya yi rijista, ya kuma nemi ƙarin bayani.

Shin kana ganin a yanzu za a iya cewa harkar rubutun adabi tana samun cigaba ne ko koma-baya?

Ba laifi, ana samun cigaba. Idan aka kwatanta da wasu shekaru a baya kaɗan, lokacin da ake yin rubutun kara-zube babu tsari, littattafan ma sam ba su da inganci sannan babu haɗin kan daƙile ayyukan batsa da su ma ake ganin marubutan Hausa ne ke yi. To, yanzu abin yana inganta. AlhamduliLlah!

Yaya alaƙa take gudana tsakanin tsofaffin marubuta da masu tasowa, wajen taimakekeniya da jagoranci?

Ba yabo ba fallasa, kadaran-kadahan. Wasu tsaffin marubutan ba su da matsala sukan ja sabbi a jikinsu su nusar da su hanyar da ya kamata su bi su zama marubuta abin sha’awa da kwatance. Wasu kuwa gaskiya akasin hakan ne, ina yawan samun ƙorafin sabbin marubutan cewa da wance da wane sun yi musu abin da bai dace ba ko kuma ma sun ƙi sauraren su gabaɗaya.

Marubuta da dama musamman maza sun fara canza sheƙa zuwa rubutun finafinai, shin me ka ke ganin ya jawo haka?

Ba shakka wannan yana da alaƙa da yadda duniyar ta sauya, rubutun fim ya fi kawo kuɗaɗe sosai sama da littafi. Sannan sauƙaƙar hanyoyin shirya fina-finan ita ta ba da gudunmawa matuƙa.

Tsakanin rubutun zube, wasan kwaikwayo da rubutun waƙa, wanne ya fi ɗaukar hankalinka?

Gaskiya na fi karkata ga rubutun zube, sai waƙa ita ma ina ɗan tavawa kaɗan.

Wanne cigaba ka ke hangen nan gaba za a samu a harkar rubutun Hausa?

Akwai cigaba sosai da zai zo a nan gaba dangane da rubutun Hausa, musamman idan muka duba yadda harshen Hausa yake ƙara bunƙasa da samun cigaba a duniya. Manyan hukumomin duniya sun lura da muhimmancin harshen har ma sun ɗaukaka shi a wasu muhimman abubuwa misali, fassarar huɗubar aikin hajji da saka harshen cikin harsunan da ake amfani da su a Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Afrika ta Yamma (ECOWAS).

Haka nan kafafen watsa labarai na duniya suna bakin ƙoƙarinsu wajen bunƙasa harkar rubutun Hausa, sanannen misali shi ne gasar Hikayata da sashen Hausa na BBC ke shirya wa marubuta mata.

Shin kana ganin ya kamata marubutan adabi su mayar da hankali wajen buga littattafan ilimi da za a yi amfani da su a makarantu?

Qwarai da gaske, ai wannan ci gaba ne sosai. Idan har marubuci zai qirqiri labarin da zai iya kawo mafita ga matsalolin al’umma, to babu shakka ya kamata ya rubuta wanda za a riƙa amfani da su sosai a makarantunmu. Kodayake a yanzun ma akwai littafan adabin da ake nazarin su a makarantu.

Wanne fata ka ke da shi ga marubuta da harkar adabi?

Fatana ga marubuta shi ne mu haɗa kanmu, mu ƙara zama tsintsiya maɗaurinmu ɗaya. Ta haka ne kowanne marubuci zai samu ɗaukaka da cigaba, haɗin kai babu abin ba ya kawowa. Fatana ga harkar adabi shi ne duk duniya lungu da saƙo ko’ina a fahimci tasirin marubuta, yadda aka ɗaukaki wasu harkoki aka ba su muhimmanci, to harkar adabi da marubuta ma a ba su wannan muhimmancin.

Wacce karin magana ce ke tasiri a rayuwarka

Mahaƙurci mawadaci.

Na gode.

Ni ma ina godiya sosai.